Zargin ta'addanci: Gwamnan Bauchi ya ƙallubalanci Ortom da ya kawo hujja

Zargin ta'addanci: Gwamnan Bauchi ya ƙallubalanci Ortom da ya kawo hujja

- Gwamna jihar Bauchi Bala Mohammed ya kallubanci Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya kawo hujjar danganta shi da ta'addanci

- Gwamna Ortom cikin wani jawabi da ya yi a ranar Litinin ya yi ikirarin cewa gwamnan Bauchin dan ta'adda ne

- Ya kuma kara wani zargin na cewa Gwamna Mohammed yana daukan nauyin makiyaya Fulani masu kisa sannan ya ce makiyaya sun yi barazana ga rayuwarsa

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya kallubalanci takwararsa na jihar Benue Samuel Ortom cewa ya kawo hujjar danganta shi da daukan nauyin ta'addanci, The Nation ta ruwaito.

Ortom ya yi zargin cewa Mohammed dan ta'adda ne kuma yana daukar nauyin makiyaya.

Ya kuma yi ikirarin cewa makiyaya sun yi barazana ga rayuwarsa, inda ya ce Mohammed za a kama idan wani abu ya faru da shi.

Kawo hujjar cewa ni dan ta'adda ne: Gwamnan Bauchi ya kallubalanci Ortom
Kawo hujjar cewa ni dan ta'adda ne: Gwamnan Bauchi ya kallubalanci Ortom. Hoto: The Nation News
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna

Sai dai a sanarwar da ya fitar a daren Laraba, hadimin gwamnan Bauchi a bangaren watsa labarai, Mukhtar Gidado, ya ce Mohammed ya bukaci Ortom ya gabatar da hujjoji kan zargin da ya yi.

Wani sashi na sanarwar ta ce, "A yunkurin na kwantar da rikicin da ya fara tashi a kasar kan korar makiyaya fulani daga jihar Ondo, mun yanke shawarar ba za mu tankawa kowa ba kan matsayar mai Girma Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed CON a kan batun.

"Amma duk da haka, ba zai yiwu ku kawar da kai bisa ikirarin da Gwamnan Benue Dr Samuel Ortom ya yi ba yayin taron manema labarai a ranar Litinin da ta gabata inda ya yi zargin cewa:

"Gwamna Bala Mohammed dan ta'adda ne kuma ya na daukan nauyin wadanda ya kira makasa makiyaya fulani.

DUBA WANNAN: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya

"Da kuma cewa ya samu wasika daga Makiyaya Fulani ne cewa za su kashe shi (Gwamna Ortom) kuma Gwamna Bala Mohammed za a kama idan wani abu ya faru da shi wato idan shi (Ortom) ya mutu."

Sanarwar ta cigaba da cewa gwamnan Bauchi ya yi mamakin yadda Gwamna da ya kira kansa dan uwansa zai kuma ce shi dan ta'adda ne.

Don haka gwamnan Bauchi ya kallubalanci Ortom ya kawo hujja kan wadannan zargin da ya yi masa.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164