Tsohon shugaban kasa IBB yayi karin haske kan hanyoyin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

Tsohon shugaban kasa IBB yayi karin haske kan hanyoyin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

- Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta shawo kan matsalolin tsaro da take fuskanta

- IBB ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 23 ga watan Fabrairu, a Minna, babban birnin jihar Neja

- Tsohon shugaban kasar ya ce an sanar da shi cewa hukumomin tsaro suna aiki tukuru don kawo karshen ta’addanci a kasar

Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce za a iya magance barazanar tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu ta hanyar yin dogon shiri.

Channels TV ta ruwaito cewa Babangida, a wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, 23 ga Fabrairu, ya ce kasar za ta iya shawo kan matsalar tsaro idan wadanda ke kan mukamai suka yi shiri yadda ya kamata.

Legit.ng ta tattaro cewa ya ce kawar da barazanar da masu satar mutane, 'yan fashi, da masu tayar da kayar baya ke yi yana bukatar babban shiri, ya kara da cewa ba shiri bane na wani dan gajeren lokaci.

Tsohon shugaban kasa IBB yayi karin haske kan hanyoyin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya
Tsohon shugaban kasa IBB yayi karin haske kan hanyoyin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Saurayi ɗan shekaru 12 ya kashe budurwar sa mai shekaru 15 a Jigawa

Janar IBB ya ce ya samu bayanai da ke nuni da cewa hukumomin tsaro na aiki tare don tsara sabbin dabaru kan yadda za a shawo kan lamarin.

Tsohon shugaban kasa IBB yayi karin haske kan hanyoyin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Tsohon shugaban kasar yayin da yake bayyana cewa ya damu da halin da kasar ke ciki, ya bukaci gwamnati da ‘yan kasa da su hada karfi don shawo kan matsalar.

A gefe guda, Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, Janar Abdulasalmi Abubakar, ya ce sulhu da tsagerun yan bindiga ba shi bane mafita daga cikin halin da ake ciki ba.

Janar AbdusSalam ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin Najeriya, yayinda suka kai msa ziyara gidansa dake Minna, jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: 2023: Hadimin Tsohon Shugaban kasa ya karyata rade-radin takara da komawar Jonathan APC

Ya yi kira ga gwamnatin jihar tayi duk mai yiwuwa domin ceto daliban makarantar GSC Kagara.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel