Harin Maiduguri: Gwamna Zulum ya kai ziyara Asibiti, ya tabbatar da mutuwar mutum 10

- Zulum ya kai ziyara asibiti, ya tabbatar da jigatan mutane 47 a harin Talata

- Farfesan ya bayyana cewa gwamnatinsa na daukan mataki kan lamarin

- Ya yi tsokaci kan kwace Marte daga hannun yan ta'addan Boko Haram

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ziyarci asibitoci biyu ranar Laraba, bayan harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai Maiduguri inda suka kashe mutane 10 kuma 47 suka jigata.

Gwamnan ya bayyana cewa yan ta'addan sun harba roka unguwannin Gwange, Adam Kolo.

A unguwar Gwange rokan ya fi hallaka mutane inda ya sauka wajen wasan yara.

Zulum yace: "Lallai abin takaici ne ga mutan Borno da gwamnatin jihar, kimanin mutane 60 abin ya shafa, 10 sun mutu."

"Ya faru sakamakon harbin da yan ta'addan sukayi ne. Mun fuskanci irin haka shekara daya da ya wuce."

Harin Maiduguri: Gwamna Zulum ya kai ziyara Asibiti, ya tabbatar da mutuwar mutum 10
Harin Maiduguri: Gwamna Zulum ya kai ziyara Asibiti, ya tabbatar da mutuwar mutum 10 Hoto: The Governor of Borno State
Source: Facebook

Source: Legit.ng

Online view pixel