Tsadar kudin wutan lantarki: Muna biyan ninki ukun abinda muke biya a baya, 'yan Najeriya
- 'Yan Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu dangane karin kudin wutan lantarki a kasar
- Sun bayyana cewa gwamnati da hukumar wutan lantarki sun yaudari 'yan Najeriya kan karin
- Hakazalika sun bayyana ra'ayoyinsu dangane da halin da ake ciki na tsadar kudin wutan lantarki
‘Yan Najeriya na ci gaba da gunaguni kan karin wuce gona da iri na kudin wutar lantarki da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta aiwatar.
NERC, wacce ta amince da karin kudin da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) ta fitar, ta ce karin ya kasance tsakanin N2 zuwa N4, amma wani bangare na masu amfani da wutar da suka sake cajin mitocin su kwanan nan, sun nace cewa karin ya haura N4.
Aminiya ta tattauna da ’yan Najeriya don gano yadda hawan ya shafi amfani da wutar lantarki da suke yi.
Jimillar mutane 494 suka halarci zaɓen kuma kashi 45.3 cikin ɗari sun bayyana cewa suna biyan ninki biyu na abin da suke biya kafin karin.
KU KARANTA: Cikin Hotuna: Gwamnan Neja ya karbi fasinjojin da suka 'yan fashi suka saka
Kusan kashi 36.4 sun lura cewa harajin ya ninka sau uku yayin da kashi 11.3 ya bayyana cewa kawai sun ɗan sami ƙari ne.
Kuma kashi 6.9 na wadanda suka amsa sun ce jadawalin karin kudin ya kasance kamar yadda yake.
Wani mai amfani da shafin Twitter, @BigMikeforyou ya bayyana cewa
“karin kudin wutar lantarki ya rubanya idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. A da mun samu kusan adadin yunit 80 a N2,000 amma yanzu 45 muke samu a N2,000. Yanzu mun daina amfani da dutsen guga da sauran kayan lantarki da ke cin wutar lantarki da yawa. ”
A wani rahoto da Aminiya ta gabatar a baya, wani mai amfani da shafin Twitter, Richard Daniel a karkashin Port Harcourt DisCo, ya ce galibi ya kan samu yunit 153.9 idan ya sayi na N5000. Don da haka, wannan ya ragu zuwa yunit 88 a yanzu, yana nuna kashi 42 cikin ɗari.
Shamsudeen Ibrahim, wani mazaunin Abuja ne a karkashin Abuja DisCo, ya ce a baya, yunit na N10,000 yakan kai yunit 386 ya zuwa watan Nuwamba amma ya samu 197 kwanan nan.
“Wannan shi ne kusan kashi 49 cikin ɗari. Ana yaudarar mu kawai cewa karin bai wuce N4 ba."
KU KARANTA: Dalilin da yasa na gwangwaje tsofaffi da kyautar awaki, in ji Dan Majalisa
A wani labarin, Hukumar Kula da Haraji ta Babban Birnin Tarayya (FCT-IRS) ta bukaci duk masu biyan haraji a cikin babban birnin kasar da su gabatar da bayanan harajinsu na shekara-shekara, tana mai cewa wannan ita ce kadai hanyar da za ta sanya garin zama kamar Dubai ko Singapore.
Dubai ce kan gaba wajen yawan yawon bude ido a duniya, a rahoton Daily Trust. A lokacin da yake zantawa da NAN a Abuja a ranar Lahadi, Abdullahi Attah, Shugaban hukumar, ya ce...
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng