Kimanin 'yan Najeriya miliyan 87 ke fama da matsanancin talauci, AfDB

Kimanin 'yan Najeriya miliyan 87 ke fama da matsanancin talauci, AfDB

- Shugaban AfDB ya bayyana cewa ana cikin matsanancin halin talauaci a kasar Najeriya

- Shugaban ya siffanta Najeriya da talauci duba da rashin aikin yin matasa a kasar ta Najeriya

- Hakazalika ya kalubalanci gwamnatin tarayya kan yadda ya kamata ta yaki talauci a kasar

Shugaban, Kungiyar Bankin Raya Kasashen Afirka, Dakta Akinwumi Adesina, ya ce kimanin mutane miliyan 87 ke rayuwa cikin matsanancin talauci a Najeriya, a rahoton Aminiya.

Ya fadi haka ne jiya a Akure yayin da yake gabatar da wata takarda mai taken “From Federal Fatherism to a Commonwealth” a matsayin laccar ƙaddamarwa a karo na biyu na Gwamna Oluwarotimi Akeredolu.

Ya ce: "Wannan talaucin da ya tabarbare" ya sanya kasar "ta kasance mai matukar fuskantar barazanar zamantakewa da siyasa" kuma ta samar da "kofa ga masu adawa da zamantakewar al'umma da daukar ma'aikata daga 'yan tawaye da 'yan ta'adda".

KU KARANTA: CBN da wasu za su haɓaka tsarin gudanar da kasuwar Bitcoin

Kimanin 'yan Najeriya miliyan 87 ke fama da matsanancin talauci, AfDB
Kimanin 'yan Najeriya miliyan 87 ke fama da matsanancin talauci, AfDB Hoto: Business Day
Asali: UGC

Ya ce talauci, wanda ke hade da manyan ayyuka da rashin ci gaba, ya haifar da "karuwar aikata laifuka, 'yan bindiga da satar mutane a Najeriya."

Dr Adesina ya ce sama da kashi 55 na matasa ba su da aikin yi, ya kara da cewa "Ta ya za ku sakawa mutanen da dakyar suke cin abinci haraji."

Ya yi fatali da tsarin tarayyar kasar na yanzu da aka gina bisa dogaro da kasafin kudi, yana mai cewa abin da kasar ke bukata shi ne mafi karfin tattalin arziki da ikon tafiyar da kasafin kudi ga jihohi.

“Batun ba na ikon cin gashin kai na jihohi ko na yanki bane, batu ne na karfin kudi da tattalin arzikin jihohi da mazabun Najeriya.

"Amurka da muka kwafa daga gareta ba ta sarrafa albarkatu a matakin jiha, a maimakon haka jihohi ke samar da mafi yawan kudaden shigar su daga haraji," in ji shi.

KU KARANTA: Shikenan: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano

A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce Najeriya ce ta fi kowacce kasa talauci a duniya, Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya yi wannan bayanin ne a lokacin da aka kaddamar da Hukumar Kula da Kare Lafiyar Jama’a a jihar ranar Talata.

Ya ce gwamnatinsa ta kafa hukumar ne don tabbatar da cewa duk shirye-shiryen kare zamantakewa an isar da su cikin hadaka, mai kunshe da ci gaba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel