Gumi ya koma limamin ƴan bindiga, ya kamata a tuhume shi, cewar wata ƙungiyar Arewa

Gumi ya koma limamin ƴan bindiga, ya kamata a tuhume shi, cewar wata ƙungiyar Arewa

- Wata kungiyar jama’a a Kaduna mai suna Southern Kaduna Peoples’ Union ta dasa ayar tambaya game da yadda Sheik Ahmad Gumi yake hulɗa da ‘yan fashi

- Kungiyar SOKAPU ta yi ikirarin cewa a yanzu Gumi ya fi damuwa da jin dadin masu aikata laifuka fiye da ganin an yi adalci ga wadanda abin ya cika da su

- Don haka kungiyar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su hanzarta bincikar ayyukan malamin

Wasu yan Najeriya sun yaba da jarumtar da Sheik Abubakar Ahmad Gumi ya yi wajen tattaunawa da 'yan fashi a arewa.

Sai dai kuma, wasu kungiyoyi sun yi tir da kiran da Gumi ya yi ga gwamnatin tarayya kan ta yi musu afuwa, daya daga cikinsu ita ce kungiyar Southern Kaduna Peoples’ Union (SOKAPU), jaridar Punch ta ruwaito.

Kakakin SOKAPU na kasa, Luka Binniyat, ya yarda cewa ya kamata hukumomin tsaro a Najeriya su binciki matsayar Gumi, wanda a cewarsa, ya zama Shugaban ruhin masu aikata laifin.

Gumi ne Shugaban ruhin yan fashi, kungiyar arewa ta dau zafi, ta yi kira ga bincikar malamin
Gumi ya koma limamin ƴan bindiga, ya kamata a tuhume shi, cewar wata ƙungiyar Arewa Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud GumI
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Bankwanan ADC da Buhari: Ƙaramar yarinya ta nuna bajinta, ta sarawa shugaban ƙasa

A nasa ra'ayin, Binniyat ya yarda cewa akwai lauje cikin nadi a tattaunawa da 'yan bindigar da suka jawo wa dubunnan mutane radadi da wahala.

Mai magana da yawun kungiyar ya ce ya ga wani bidiyo inda Gumi ya yi ikirarin cewa 'yan bindigar sun fusata saboda sojoji wadanda ba Musulmi ba ne ke kashe su.

Binniyat ya ce:

"Ya gaya musu cewa sojojin da ke kashe su ba sojoji Musulmi bane. Ya ce idan sun far wa wata al'umma a cikin 'daukar fansa', ya kamata su zabi wadanda suke hari da kyau. Ya nuna kyama ga yadda wata kungiyar masu garkuwa da mutane suka yi ram da wasu matafiya kuma a cikin su akwai wata mace a cikin hijabin Musulunci dauke da karamin jariri.

"Don haka, kun gani, malamin yana maida kansa kamar jagoran ruhohin 'yan fashin. Idan' yan bindigar sun cancanci a tattauna da su to yana tare da doka don ayi adalci."

Ya yi mamakin dalilin da ya sa Gumi "ba ya sha'awar adalci da biyan diyya ga dubunnan wadanda suka tsira daga sharrinsu, amma ya damu da jin daɗi da 'yancin masu aikata muggan ayyuka."

KU KARANTA KUMA: Ba dan ta'adda bane: FKK ya ambaci gwamnan arewa da ya taimaki Jonathan ya zama shugaban kasa bayan 'Yar'adua

A wani labarin kuma, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya ce abokin aikinsa, gwamnan jihar Bauchi, Bala A. Mohammed, za a kama idan har aka hallaka shi.

Daily Trust tace Samuel Ortom ya yi kira ga takwaransa, Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya nemi afuwar mutane a kan wasu kalamai da ya yi.

Gwamnan Benuwai ya ce muddin Bala Abdulqadir Mohammed bai bada hakuri ba, dole jama’a za su yarda cewa da shi ake kokarin ganin bayansu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel