Ba dan ta'adda bane: FKK ya ambaci gwamnan arewa da ya taimaki Jonathan ya zama shugaban kasa bayan 'Yar'adua

Ba dan ta'adda bane: FKK ya ambaci gwamnan arewa da ya taimaki Jonathan ya zama shugaban kasa bayan 'Yar'adua

- Femi Fani-Kayode ya kare gwamnan Bauchi Bala Mohammed

- Tsohon ministan na sufurin jiragen sama ya bayyana Bala a matsayin dan Najeriya mara kabilanci kuma mutum mai hazaka

- FFK, kamar yadda ake kiran shi, ya ce zai zama "rashin kyautuwa da wauta" a bayyana gwamnan na Bauchi a matsayin dan ta'adda

Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya tsoma bakinsa cikin takaddamar da ke tsakanin Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da Rotimi Akeredolu na Ondo.

Gwamnonin biyu na ta yamutsa gashin baki a kafofin yada labarai game da rikicin kabilanci da rashin tsaro a yankin kudu maso yammacin kasar.

KU KARANTA KUMA: FG ta bayyana ainahin dalilin da ya sa kungiyar Boko Haram ta ki sakin Leah Sharibu

Ba dan ta'adda bane: FKK ya ambaci gwamnan arewa da ya taimaki Jonathan ya zama shugaban kasa bayan 'Yar'adua
Ba dan ta'adda bane: FKK ya ambaci gwamnan arewa da ya taimaki Jonathan ya zama shugaban kasa bayan 'Yar'adua Hoto: @Bauchigov @RealFFK
Asali: Twitter

Rikicin ya fara ne lokacin da Bala ya yi tsokaci a kan daukar makamai kirar AK-47 da makiyaya ke yi, lamari mai cike da rudani da Akeredolu ya bayyana a matsayin wanda zai iya rura wutar rikicin kabilanci.

Da yake bayyana matsayinsa a kan rikicin a wani sako a shafin Twitter a ranar Litinin, 22 ga Fabrairu, Fani Kayode ya ce duk da cewar ya saba "a lokuta da dama cikin shekaru" da Bala, ba zai taba yarda da ra'ayin mutanen da ke kiransa "dan ta'adda ba."

Tsohon ministan na jiragen sama ya bayyana hakan a matsayin "rashin kyautawa da wauta".

Ya bayyana Bala a matsayin "mutumin da ya tsaya wa 'yan kudu da Kiristoci kamar yadda yake tsayawa Musulmin Arewa."

FFK ya kuma bayyana cewa in ba don Bala ba, da Goodluck Jonathan ba zai zama shugaban Najeriya ba bayan da tsohon maigidansa Umar Musa Yar'adua ya mutu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta san inda ‘Yan bindiga su ke boyewa inji Sheikh Ahmad Gumi

A wani labarin kuma, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya ce abokin aikinsa, gwamnan jihar Bauchi, Bala A. Mohammed, za a kama idan har aka hallaka shi.

Daily Trust tace Samuel Ortom ya yi kira ga takwaransa, Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya nemi afuwar mutane a kan wasu kalamai da ya yi.

Gwamnan Benuwai ya ce muddin Bala Abdulqadir Mohammed bai bada hakuri ba, dole jama’a za su yarda cewa da shi ake kokarin ganin bayansu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel