Bankwanan ADC da Buhari: Ƙaramar yarinya ta nuna bajinta, ta sarawa shugaban ƙasa

Bankwanan ADC da Buhari: Ƙaramar yarinya ta nuna bajinta, ta sarawa shugaban ƙasa

- ‘Yar Mohammed Abubakar, tsohon dogarin Shugaba Buhari, ta ja hankali yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga Shugaban kasar

- An gano karamar yarinyar a cikin wani hoto da ya yi fice tana sarawa Shugaban kasar a Villa a gaban iyayenta

- Abubakar, dogarin shugaban kasa mafi dadewa a Najeriya, zai fita waje don yin wani kwas da zai kai shi ga mukamin Birgediya Janar

Dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado, Kanal Mohammed Abubakar, ya gayyaci iyalansa zuwa fadar shugaban kasa a ranar Talata, 23 ga watan Fabrairu, yayinda yake shirin mika mulki ga magajinsa.

ADC din mai barin gado ya shirya don gabatar da wata wasikar godiya ga Shugaba Buhari yayinda ya mika mukaminsa ga magajinsa.

KU KARANTA KUMA: Mawaƙi Rarara ya gwangwaje tsoffin ƴan wasan Hausa da kyautar N50,000 kowanne

Sai dai kuma, karamar yar Abubakar ta ja hankali a taron yayinda ta nuna kwarin gwiwa a shirinta na haduwa da Shugaba Buhari.

Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar
Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar Hoto: @BayoOmoboriowo
Asali: Twitter

A cewar Bayo Omoboriowo, mai hoton shugaban kasa, tsohon dogarin ya bude ofishin Shugaba Buhari don sanar masa da cewar iyalinsa sun iso.

Sai dai, yarsa wacce ta kasance cikin farin cikin haduwa da shugaban kasar ta so rugawa ciki tare da shi amma sai ya ce mata ta jira shi a baya.

Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar
Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar Hoto: @BayoOmoboriowo
Asali: Twitter

Ga mamakinta, sai Shugaba Buhari wanda ya ji muryarta ya je bakin kofar don haduwa da ita maimakon gayyatarta ciki.

Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar
Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar Hoto: @BayoOmoboriowo
Asali: Twitter

Yarinyar ta gaza boye farin cikinta har aka gama taron sannan ta dungi tikar rawa, Oboriowo ya bayyana.

KU KARANTA KUMA: Ba dan ta'adda bane: FKK ya ambaci gwamnan arewa da ya taimaki Jonathan ya zama shugaban kasa bayan 'Yar'adua

Sannan ta sarawa shugaban kasar bayan mahaifinta ya gama gabatar da wasikar godiyar tasa.

Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar
Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar Hoto: @BayoOmoboriowo
Asali: Twitter

Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar
Yar dogarin Buhari mai barin gado ta burge yayinda mahaifinta ya gabatar da wasikar godiya ga shugaban kasar Hoto: @BayoOmoboriowo
Asali: Twitter

A baya mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya canza dogarinsa wanda akafi sani da ADC, kuma ya zabi sabon ADC, Channels TV ta jiyo daga fadar shugaban kasa.

Laftanan Kanal Y. M Dodo zai maye Kanal Muhammed Abubakar, wanda ya ke tsare Buhari tun 2015.

A cewar majiyoyin, Kanal Abubakar zai ajiye aikinsa ne saboda halartan wani kas domin ya samu karin girma zuwa matsayin Birgediya Janar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel