Wanda za a cafke idan aka hallaka ni shi ne Gwamnan Bauchi – Gwamna Ortom

Wanda za a cafke idan aka hallaka ni shi ne Gwamnan Bauchi – Gwamna Ortom

- Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya sake dura ta kan Bala Mohammed

- Samuel Ortom ya ce idan aka kashe shi, mutane su cafke Gwamna Mohammed

- Gwamna Ortom ya ce idan har ya mutu, to mutane su cafke Bala Mohammed

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya ce abokin aikinsa, gwamnan jihar Bauchi, Bala A. Mohammed, za a kama idan har aka hallaka shi.

Daily Trust tace Samuel Ortom ya yi kira ga takwaransa, Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya nemi afuwar mutane a kan wasu kalamai da ya yi.

Gwamnan Benuwai ya ce muddin Bala Abdulqadir Mohammed bai bada hakuri ba, dole jama’a za su yarda cewa da shi ake kokarin ganin bayansu.

Samuel Ortom ya bayyana haka ne da yake magana da ‘yan jarida a garin Makurdi, ya ce abin takaici ne a ji gwamnan Bauchi ya na kare ‘yan bindiga.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Komai zai dawo dai-dai, ya lafa a wata 2 - Lawan

Ortom yake cewa makiyayan da su ka shigo Najeriya daga kasar waje sun kashe al’umma barkatai, sannan sun jefa jama’a cikin bakin ciki a fadin kasar.

Gwamnan na jihar Benuwai ya kara yin kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana wadannan makiyaya a matsayin ‘yan ta’adda.

Mista Ortom yake cewa duk wani wanda yake bin dokar hukuma, zai iya yin harkokinsa a Benuwai

Da aka tuntubi wani hadimin gwamnan Bauchi, Mukhtar Mohammed Gidado, ya ki cewa uffan a game da kalaman da su ke ta fito wa daga bakin na Ortom.

Wanda za a cafke idan aka hallaka ni shi ne Gwamnan Bauchi – Gwamna Ortom
Gwamna Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Yuguda, ya ce ba ayi wa Fulani adalci

Wani babban jami’in gwamnatin jihar Bauchi ya yi magana da ‘yan jarida, ya ce Bala Mohammed ba zai fito ya maida martani ga gwamna Samuel Ortom ba.

A farkon makon nan ne mu ka ji cewa rabuwar kai tsakanin gungun Miyagu ya sa aka gagara ceto ‘yan makarantar sakadare ta GSSS Kagara da aka sace.

Dalibai 27 da Ma’aikata 15 na GSSS Kagara da aka sace su na tsare a hannun ‘Yan bindiga har yau.

A wata hira da aka yi da Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa ana kokarin shawo kan ‘yan bindigan su fito da mutanen da su ka dauke daga makarantar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel