Yan Boko Haram sun kai hari Maiduguri, sun hallaka mutane akalla 15

Yan Boko Haram sun kai hari Maiduguri, sun hallaka mutane akalla 15

- Bayan shekara da shekaru, yan Boko Haram sun kai hari birnin Maiduguri

- Akalla mutane 17 suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai

- Hakan ya biyo bayan kwato Marte daga hannun yan ta'addan Boko Haram

HumAngle ta ruwaito cewa jami'an Sojin Najeriya sun yi artabu da yan ta'addan Boko Haram da suka kai mumunan harin Maiduguri, birnin jihar Borno da yammacin Talata, 23 ga Febrairu, 2021.

Yan ta'adda sun yi kokarin shiga birnin ne inda suka rika harbi kuma suka hallaka mutane.

Sun yi kokarin shiga Maiduguri ne ta yankin Kaleri, kusa da jami'ar Maiduguri.

A cewar HumAngle, rokokin da yan ta'addan suka harba yayi sanadiyar halakan rayukan akalla 17.

"Muna shirin Sallan Magariba ne aka harbo roka kan mutane kusa da Masallaci," cewar Mallam Musa, wani mazaunin Gwange Burburwa, inda aka kai harin.

Wani mazaunin, Mele Gana, ya bayyana cewa "Rokan ya kashe mutane uku kuma da yawa sun jikkata."

A cewar wani jami'in gwamnatin jihar wanda ya bukaci a sakaye sunansa, mutane 17 suka mutu kuma 43 sun jigata.

KU KARANTA: Minista ta dakatar da Sarki saboda ‘hada kai da masu garkuwa da mutane’ a Abuja

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Maiduguri, sun hallaka mutane akalla 15
Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Maiduguri, sun hallaka mutane akalla 15
Source: Original

DUBA NAN: 'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC

Da farko hankalin mutane a Maiduguri, birnin jihar Borno, ya tashi sakamakon karan tashin bama-bamai da suke ji da yammacin Talata, 23 ga watan Febrairu, 2021.

Mazaunan sun bayyana cewa tun karfe 6 na yamma suka fara jin kararrakin.

"Ina hanyar zuwa Masallaci na fara jin karan tashin Bam, sannan na fara jin harbe-harbe," daya daga cikin mazaunan yace.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel