Minista ta dakatar da Sarki saboda ‘hada kai da masu garkuwa da mutane’ a Abuja
- Ramatu Tijjani Aliyu ta bada sanarwar dakatar da Sarkin Anagada a Abuja
- Ministar birnin Abujar tace ana zargin Basaraken da ba ‘Yan bindiga taimako
- An bada wannan sanarwar ne a wajen wani taron gaggawan da aka yi a jiya
Karamar Ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Tijjani Aliyu, ta dakatar da Sarkin kasar Anagada da ke karamar hukumar Gwagwalada.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana zargin Mai martaba Alhaji Alhassan Musa ne da taimaka wa masu garkuwa da mutane a babban birnin tarayya.
Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ta bayyana haka a wajen taron tsaro na gaggawa da aka shirya da masu sarautar gargajiya da sarakunan da ke Abuja a jiya.
Haka zalika dukkanin shugabannin kananan hukumomi shida na birnin tarayya sun halarci wannan taro.
KU KARANTA: Wani Basarake a jihar Ogun ya na goyon bayan Tinubu a 2023
Ministar ta bayyana cewa sun dauki matakin dakatar da Sarkin Anagada ne sakamakon rahotanni da su ka samu cewa ya na hada-kai da ‘yan bindiga.
Sai dai Ministar ba ta bayyana ta yadda Basaraken yake taimaka wa masu garkuwa da mutanen ba, sannan ba a bayyana tsawon dakatarwar da aka yi masa ba.
Ramatu Tijjani Aliyu ta tabbatar wa mazauna garin Abuja da kewaye cewa su na yin bakin kokarinsu na ganin cewa sun tsare rai da dukiyar al’ummarsu.
A karshe Ministar birnin tarayyar ta yi kira ga jama’a su zauna lafiya, sannan su bude idanunsu, domin sa ido saboda miyagun da su ke aika barna iri-iri a Abuja.
KU KARANTA: Diyar Atiku Abubakar ta sabunta rajistar APC
Tijjani Aliyu ta yi kira ga mazauna birnin tarayya Abuja da kewaye da su kai kara zuwa ofishin ‘yan sanda da ke kusa da su da zarar sun ga wani bakon lamari.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce zama da yake yi da 'yan bindiga ba wani abu ba ne, hakan na zuwa ne bayan ana ta tambayarsa yadda yake bi ya na hadu wa da miyagun.
Ahmad Gumi yake cewa jami’an tsaro su na ganin ‘Yan bindiga ta jirgin sama, sai dai ya ce sun yi hankali ne, sun daina tunkarar wadannan tsageru gaba-da-gaba.
Shehin Malamin ya ce Gwamnatin Tarayya ma ta san duk inda wadannan miyagu su ke.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng