Kawai gwamnati ta kame Sheikh Gumi ta bincikeshi kan hada kai da 'yan bindiga, wasu 'yan Najeriya

Kawai gwamnati ta kame Sheikh Gumi ta bincikeshi kan hada kai da 'yan bindiga, wasu 'yan Najeriya

- Wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu kan da'awar Gumi na shiga daji wajen 'yan bindiga

- Sun nemi gwamnati ta gaggauta kame malamin tare da yi masa tambayoyi kan mafakar 'yan bindiga

- Hakazalika wasu suna ganin malamin yana da kyakkyawar masaniya dagane da inda 'yan bindigan suke

'Yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba da umarnin kamawa da binciken shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, kan mu'amalarsa da 'yan bindiga a kasar, The Punch ta ruwaito.

A baya, an ga Sheikh Gumi a cikin hotuna yana tattaunawa da wasu gungun 'yan bindiga a dazukan Zamfara, Neja da sauran jihohi. Ya kuma bayar da shawarar a yi afuwa ga 'yan fashi kamar yadda aka yi wa' yan bindiga a yankin Neja Delta.

Mun ruwaito cewa, Sheikh Gumi, a ranar Litinin, ya ce 'yan bindigar sun kashe mutane "kalilan" ne kawai cikin rashin sani, ya kara da cewa sun kashe ne don "ramuwar gayya".

Kalaman Sheikh Gumi na baya-bayan nan sun ja hankali a shafukan sada zumunta inda yawancin masu amfani dasu suka bayyana shi a matsayin kakakin 'yan bindiga a kasar.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace surukar shahararren dan kasuwa Dahiru Mangal

Kawai gwamnati ta kame Sheikh Gumi ta bincikeshi kan hada kai da 'yan bindiga, 'yan Najeriya
Kawai gwamnati ta kame Sheikh Gumi ta bincikeshi kan hada kai da 'yan bindiga, 'yan Najeriya Hoto: The Gaurdian
Source: UGC

Wani mai amfani da shafin Twitter, @FolarinCharles, ya nuna kaduwa da kalaman malamin.

“Abin da yake fadi abin mamaki ne. Ya ce 'yan bindigan na neman a biya kudin fansa ne kawai kuma yawanci kashe-kashen su cikin rashin sani ne. Haba, menene 'yan bindigan ke yi wa waɗanda ba za su iya biyan fansa ba? Suna kawai kashe su ba tare da waiwaye ba,”

@YourfavLollipop ya zargi Malamin inda yake cewa:

"Idan da nan Amurka ce, da an jefa wannan mutumin gidan yari… shi ne mai kula da su,"

Wani, @Greatrufus1, ya bayyana cewa:

“Sheikh Gumi ya dauki matsayin ubangida da kuma kakakin 'yan bindiga a fadin Najeriya. Bari mu ga inda hakan ke jagorantar su. "

@UncleGoodBoy ya ce,:

"Idan da Gumi dan Kudu ne, da DSS ta kama shi."

Hakanan, wasu masu amfani da Facebook ba su ji dadin maganganun da ayyukan malamin na baya-bayan nan ba, suna kira ga hukumomin tsaro da su kamo shi nan take don amsa tambayoyi.

Iyamu Moses yayi tsokaci:

“Najeriya ta kare. Don har yanzu wannan mutumin yana ci gaba da walwala bayan ganawa da masu kisan kai da 'yan ta'adda, hakan ya nuna cewa Najeriya na cikin rudani matuka. ”

Jean-Philips Aka ya ce:

"Ya kamata a binciki wannan mutumin, a bayyane yake ya san abubuwa da yawa game da wadannan mutane."

A nata bangaren, Ann Chiagolum, ta bukaci gwamnati da ta

“dauki wannan Shehin malamin don sake murmurewa kafin lokaci ya kure.”

KU KARANTA: Rabuwar kai tsakanin 'yan bindiga ne ya jawo jinkirin sake daliban GSC Kagara

A wani labarin, Shahararren malamin addinin Musuluncin nan, Ahmad Gumi, ya ce 'yan fashin da ya hadu da su a jihar Neja sun musanta labarin sace dalibai 27 na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati (GSC), da ke Kagara, TheCable ta ruwaito.

Shehin malamin ya kuma ce ba ya cikin tattaunawar sakin daliban, kawai ya hadu da 'yan fashin ne don ya nisanta su da aikata laifi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel