Rabuwar kai tsakanin 'yan bindiga ne ya jawo jinkirin sake daliban GSC Kagara

Rabuwar kai tsakanin 'yan bindiga ne ya jawo jinkirin sake daliban GSC Kagara

- Majiya ta bayyana cewa, jinkirin sakin dalibai da malamansu a matsayin rashin jituwa

- Fitaccen malamin addinin Islama, Gumi ma ya shaida rashin jituwa tsakanin 'yan bindigan

- Hakazalika, ya bayyana babu takamamman ranar da za a sako daliban da malaman GSC Kagara

Akwai alamu masu karfi a ranar Litinin cewa rashin jituwa tsakanin ‘yan fashi a jihar Neja na jinkirta sakin daliban 27 da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati 15, da aka sace a ranar Laraba.

Wata majiya daga gwamnati, wacce ta bayyana wa jaridar Punch, ta ce 'yan bindigar da suka yi garkuwar ba su amince da tattaunawar da sukayi da wakilan gwamnatin ba.

An samu sabani kan sakin mutanen da aka sace a ranar Lahadi. A safiyar ranar Lahadi, jami’an jihar Neja da majiyoyin tsaro sun ce an sako wadanda aka sace kuma suna kan hanyarsu ta shigowa Minna, babban birnin jihar.

Amma daga baya, Gwamnan jihar, Sani Bello, ya ce har yanzu wadanda akayi garkuwa da su din suna tsare.

KU KARANTA: Cikin Hotuna: Gwamnan Neja ya karbi fasinjojin da 'yan fashi suka saka

Rabuwar kai tsakanin 'yan bindiga ne ya jawo jinkirin sake daliban GSC Kagara
Rabuwar kai tsakanin 'yan bindiga ne ya jawo jinkirin sake daliban GSC Kagara Hoto: BBC Hausa
Asali: Twitter

Majiyar gwamnatin, wacce ta yi magana da manema labarai, ta ce, “Akwai rarrabuwa kai a tsakanin 'yan bindigan. Ana lallashin wadanda suka yi garkuwar da su saki wadanda suka sace."

Hakanan, wani fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, wanda ke da hannu a tattaunawar sakin wadanda aka sacen, ya bayyana jinkirin sakin su.

Gumi, a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, ya ce 'yan bindigar da ke rike da dalibai 42 da ma'aikata 15 na GSC Kagara har yanzu ana lallashin su su sake su.

Ya ce, “Na tabbata za a sake su. Ina da tabbacin hakan. Amma ba za mu iya cewa ga takamaiman ranar ba. Ba mu da hanyar samun waɗancan mutane tun lokacin da muka bar wurin.

"Amma muna fatan cewa zasu gamsu tunda suna son zaman lafiya kuma suna burin hakan. Na yi imani zai yi nasara.

“Suna tattaunawa a tsakanin su - na kwarai da marasa kyau. Suna kokarin shawo kansu, kuma na yi imanin za su yi hakan.”

KU KARANTA: Na tabbata daliban makarantar Kagara na dajin Birnin Gwari, in ji Gwamna Matawalle

A wani labarin, Shahararren malamin addinin Musuluncin nan, Ahmad Gumi, ya ce 'yan fashin da ya hadu da su a jihar Neja sun musanta labarin sace dalibai 27 na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati (GSC), da ke Kagara, TheCable ta ruwaito.

Shehin malamin ya kuma ce ba ya cikin tattaunawar sakin daliban, kawai ya hadu da 'yan fashin ne don ya nisanta su da aikata laifi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel