Gumi: ‘Yan bindigan da na hadu da su sun musanta sace daliban Kagara
- Babban malamin addinin musulunci dake tattaunawa da 'yan fashi ya bayyana ainihin tattaunawarsu
- Malamin yace, 'yan fashin da ya hadu dasu basu da hannu wajen sace dalibai da malaman GSC Kagara
- Malamin yace sai dai shugaban kungiyar 'yan fashin ya alkawarta gano inda suke domin a sake su
Shahararren malamin addinin Musuluncin nan, Ahmad Gumi, ya ce 'yan fashin da ya hadu da su a jihar Neja sun musanta labarin sace dalibai 27 na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati (GSC), da ke Kagara, TheCable ta ruwaito.
Shehin malamin ya kuma ce ba ya cikin tattaunawar sakin daliban, kawai ya hadu da 'yan fashin ne don ya nisanta su da aikata laifi.
A ranar Laraba ne wasu 'yan bindiga suka kai hari GSC Kagara da ke karamar hukumar Rafi a Neja, inda suka yi awon gaba da mutane 41 galibinsu dalibai da ma'aikatan makarantar.
Kwana guda bayan harin, Gumi, wanda aka san shi da samun damar tattaunawa da 'yan fashin, ya hadu da wasu daga cikinsu a cikin wani sanannen daji a Neja kuma, a gidan gwamnatin jihar, ya nemi a yi musu afuwa.
KU KARANTA: Ku biya harajinku idan kuna son Abuja ta koma kamar Dubai, Hukumar Haraji
A hirar da ya yi da THISDAY, malamin ya ce haduwar da ya yi da shugabannin ‘yan fashin na zaman lafiya ne kawai kuma ba shi da wata alaka da satar mutanen.
“Ni ba na cikin tattaunawar. Mun dai sadu da wasu daga cikin wadannan tsagerun (a jihar Neja), ina kokarin shawo kan su da daina aikata laifin," kamar yadda aka ruwaito shi yana cewa.
“Mun tambaye su (‘ yan fashin) game da abin da ya faru sai suka ce sun san kungiyar da ta sace motar bas din sai suka ce za su shiga tsakani don ganin an sake su.
“Amma ga yaran (makarantar), sun ce ba su san wanda ya yi ba saboda lokaci ya yi kusa da za su sani. Waɗannan ƙungiyoyin da muka sadu da su na iya samun matsala tare da rukunin ɓarnata.”
Gumi ya kuma ce tuni aka shirya aikin wanzar da zaman lafiya kafin yanzu kuma satar daliban wata kila "don nuna kin amincewarsu da zaman lafiya" da wasu kungiyoyi suka balle.
"Mutanen da na hadu da su ba su ne suka sace daliban ba," in ji malamin, amma ya kara da cewa "babban kwamandan kungiyar da muka hadu da shi ya yi alkawarin cewa zai binciko wadanda suka sace yaran sannan a sake su." ya kara da cewa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gargadi masu tada rikicin addini a jihar Gombe
A wani labarin, Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta yi nasarar tabbatar da sakin dukkan fasinjojin da aka sace na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja. Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da sakin dukkan fasinjojin da aka sace daga motar hukumar shige da fice ta jihar Neja.
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da hakan ta shafin Twitter a ranar Lahadi.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng