Na tabbata daliban makarantar Kagara na dajin Birnin Gwari, in ji Gwamna Matawalle
- Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa, daliban Kagara suna dajin jihar Kaduna
- Gwamnan ya bayyana hakane a cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels
- Gwamnan ya kuma bayyana bukatar hadin kai tsakanin hukumomi don inganta tsaro
A ci gaba da hasashe da neman inda aka boye dalibai da malamansu na makarantar sakandaren kimiyya ta Kagara, gwamnan jihar Zamfara ya shaidawa manema labarai inda aka boye su.
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana inda 'yan bindiga ke boye da daliban Sakandaren Kimiyya ta Kagara, wadanda aka sace da sanyin safiyar ranar Laraba da ta gabata.
Da yake magana da kafar talabijin ta Channels TV a yammacin Lahadi, gwamnan ya ce ɗaliban tare da sauran wadanda aka sace na cikin wani yankin jihar Kaduna.
KU KARANTA: Saura kwanaki 10 allurar rigakafin Korona ta iso Najeriya, Ministan Lafiya
"An hangi ɗaliban Kagara a kusa da yankin Birnin Gwari da ke Kaduna kuma na yi imanin nan gaba kaɗan za su koma gida," a cewar gwamnan.
Gwamna Matawalle ya sake nanata batun haɗin kai tsakanin mahukunta, abin da ya ce ya yi imanin shi ne sirrin nasarar samun galaba kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.
A daren Talata ne 'yan bindiga suka shiga makarantar ta Kagara da ke Jihar Neja sanye da kakin sojoji, inda suka kashe ɗalibi ɗaya sannan suka yi awon gaba da mutum 42, ciki har da ɗalibai da malamansu da iyalai da kuma ma'aikata.
KU KARANTA: Ku biya harajinku idan kuna son Abuja ta koma kamar Dubai, Hukumar Haraji
A wani labari, Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta yi nasarar tabbatar da sakin dukkan fasinjojin da aka sace na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja.
Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da sakin dukkan fasinjojin da aka sace daga motar hukumar shige da fice ta jihar Neja. Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da hakan ta shafin Twitter a ranar Lahadi.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng