Cikin Hotuna: Gwamnan Neja ya karbi fasinjojin da 'yan fashi suka saka
- Gwamnan jihar Neja ya sanar da sake fasinjojin da aka sace a hanyar zuwa Minna
- A baya dai an sace fasinjojin ne kafin daga bisani aka sace wasu dalibai a Kagara
- A halin yanzu gwamnati ta karbi wadanda aka saka mutum 53 cikin koshin lafiya
Gwamnatin jihar Neja ta karbi faasinjoji 53 da aka sace makon da ya gabata a kan hanyarsu ta komawa garin Minna.
Gwamnatin jihar ta wallafa tabbacin sakin fasinjojin a shafinta na Twitter tare da nuna hotunan fasinjojin tare da gwamnan a cikin wani katafaren dakin taro.
KU KARANTA: Ku biya harajinku idan kuna son Abuja ta koma kamar Dubai, Hukumar Haraji
Zuwa yanzu ana ci gaba da tsammanin sakin wasu dalibai da malamansu da aka sace a wata makarantar sakandare dake Kagara a jihar ta Neja.
Wani jita-jita nata yawo a kafafen sada zumunta cewa an saki daliban a jiya Lahadi. Sai dai gwamnan a tsakar daren jiya ya bayyana cewa zunzurun karya ce labarin cewa an sako daliban da malamansu.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gargadi masu tada rikicin addini a jihar Gombe
A wani labarin, Da farko mun kawo muku cewa an sako mutane 42 da yan bindiga suka sace daga kwallejin kimiyya na gwamnati da ke Kagara a jihar Niger, bisa rahoton The Nation.
Wadanda aka sace sun hada da dalibai 27, ma'aikata 3 da kuma iyalan ma'aikatan su 12. Majiyoyi sun ce wadanda aka sace din suna kan hanyarsu na komawa Minna a yanzu.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng