Hana kiwo a fili bazai magance rikicin makiyaya da manoma ba, shugaban gwamnoni

Hana kiwo a fili bazai magance rikicin makiyaya da manoma ba, shugaban gwamnoni

- Gwamnan jihar Ekiti ya bayyana cewa ba hana kiwo a fili bane mafita ga rikicin yankin

- Ya siffanta rikicin makiyaya da manoma a matsayin rikicin da ba zai kare ba sai an gyara

- Ya bukaci gwamnati da ta tallafawa makiyaya kamar yadda ake tallafawa manoma a kasar

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce haramtacciyar dokar hana kiwo a fili ba tare da kawo wata hanya ga makiyaya ba ba za ta kawo karshen rikice-rikicen manoma da makiyaya a kasar ba.

Ya fadi haka ne a daren jiya a gidan talabijin din Channels Television a shirin Sunday Politics, wanda wakilin Daily Trust ya shaida.

“Duk gwamnoninmu sun amince cewa dole ne mu bi hanyoyin zamani na kiwo da kiwo a fili da sauran ayyukan da za su kawo ci gaba.

"Dole ne mu rungumi shirinmu na sauya dabbobinmu wanda zai iya hadawa da amfani da kiwo da sauran wuraren kiwo da ke da kariya."

KU KARANTA: Tsadar kudin wutan lantarki: Muna biyan ninki ukun abinda muke biya a baya, 'yan Najeriya

Hana kiwo a fili bazai magance rikicin makiyaya da manoma ba, shugaban gwamnoni
Hana kiwo a fili bazai magance rikicin makiyaya da manoma ba, shugaban gwamnoni Hoto: Gallaxy TV Online
Asali: UGC

“Mun kuma yarda da gaskiyar cewa wannan ba zai faru ba a lokaci daya domin hakan ba zai faru ba cikin dare daya.

“Muna bukatar samun tsayayyen tsari wajen tabbatar da cewa an kawar da kiwo a fili kuma an dauki matakan kula da dabbobin zamani ta jihohi.

"Kuma dole ne mu tallafawa makiyayan yadda muke tallafawa noman rogo da manoman da ke noman shinkafa ta hanyar shirin bashi mai sauki.

"Dole ne mu tallafawa makiyaya da wadanda ke son shiga cikin kiwon dabbobi na zamani," in ji shi.

Fayemi ya ce jinkirin gurfanar da makiyaya da suka aikata laifuka ya sanya mutane da yawa suka yi amannar cewa jihar na kare makiyaya.

Ya yi kira da a dauki 'yan sandan jihohi domin baiwa gwamnoni damar "sanya 'yan sandan jihohinsu yadda ya kamata."

KU KARANTA: Sanatan Neja yayi kira ga dokar ta baci bayan sace daliban GSSS Kagara

A wani labarin, Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da kalubalen tattalin arziki, yanzu kuma dillalan shanu na barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar.

Hadaddiyar kungiyar dillalan abinci da shanu ta Najeriya (AFUCDN) ta nuna rashin jin dadin ta da cewa ana kashe mambobinta a sassa daban-daban na kasar. \

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel