Sanatan Neja yayi kira ga dokar ta baci bayan sace daliban GSSS Kagara
- Majalisar Dattijai a Najeriya ta bayyana bukatar sanya dokar ta baci kan tsaro a Neja
- Kudurin da wani sanata daga jihar Neja ya mika, ya karbu a wurin abokan aikinsa
- Hakazalika ya yi wata babbar tambaya kan cewa za a bar 'yan Najeriya su rike makami ne
Majalisar dattijai, a ranar Laraba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da, cikin gaggawa, ya sanya dokar ta baci kan tsaro sakamakon sace ma’aikata da dalibai a wata makaranta a Niger.
Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Muhammed Sani Musa (APC, Neja) ya gabatar wanda ya ja hankalin abokan aikinsa kan sace wasu dalibai da ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, Jihar Neja, da misalin karfe 2 na daren Laraba.
A jawabinsa na Sanata Musa ya ce duk da cewa jami'an tsaro sun fara aikin ceto don ganin an sako wadanda lamarin ya rutsa da su, amma har yanzu ba a san inda suke ba.
KU KARANTA: An kashe mana mutane sama da 23 a rikicin Ogun, in ji Sarkin Fulani
Legit.ng Hausa ta gano cewa lamarin ya faru ne sa’o’i 48 bayan sace wasu fasinjoji 21 da ke kan hanyarsu ta zuwa Minna, babban birnin jihar Neja rana tsaka, kamar yadda ta ruwaito a baya na faruwar lamarin.
Sanata Muhammad Bima Enagi (Neja ta Kudu) ya ce yawan kashe-kashe da sace-sacen mutane a kasar ya nuna cewa gwamnati kamar ta nuna gazawa wajen magance matsalar rashin tsaro.
"Shin muna bukatar gyara kundin tsarin mulki domin baiwa 'yan kasa damar daukar makami don kare kawunansu ne?" sanatan ya tambayi abokan aikinsa.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ce yawaitar sace-sacen yara ’yan makaranta a harabar makarantar zai yi mummunan tasiri kan yardar iyaye na tura ’ya’yansu makaranta.
Ya bukaci hukumomin tsaro da su bullo da dabarun tsaron makarantu, a rahoton Daily Trust.
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Bazan biya kudin fansa ba ko kobo, Gwaman Neja
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da sace dalibai da ma'aikatan makarantar GSSS dake Kagara, jihar Neja a ranar Talata 16 ga watan Fabrairu.
Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya wallafa jawaban shugaban kasan a shafinsa na Facebook yau Laraba da misalin karfe 11:44 na safe.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng