Yanzun nan: Gwamnatin Niger ta samu nasarar kubutar da fasinjoji da 'yan fashi suka sace

Yanzun nan: Gwamnatin Niger ta samu nasarar kubutar da fasinjoji da 'yan fashi suka sace

- Gwamnatin jihar Neja ta bayyan cewa, ta samu nasarar kubutar da wadanda aka sace

- Gwamnatin tace fasinjoji da aka sace a makon jiya ne suka kubutu bayan da aka sace su

- Fasinjojin an sace su ne a hanyar su ta zuwa Minna daga wani yankin na jihar Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta yi nasarar tabbatar da sakin dukkan fasinjojin da aka sace na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja.

Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da sakin dukkan fasinjojin da aka sace daga motar hukumar shige da fice ta jihar Neja.

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da hakan ta shafin Twitter a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana

"Muna farin cikin sanar da jama'a game da sakin fasinjojin NSTA da aka sace mako guda da ya gabata yayin da suke komawa Minna kan hanyar Minna-Zungeru," kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Sanarwar gwamnan ta zo ne kwanaki bakwai bayan wasu ‘yan bindiga sun sace a kalla matafiya 30 a kan babbar hanyar Tegina-Zungeru a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Jami'an kungiyar direbobin yankin sun ce wadanda lamarin ya rutsa da su na tafiya ne a cikin motar bas ta Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja (NSTA) lokacin da 'yan fashin suka ci karo da su.

‘Yan bindigar sun kuma kashe wasu‘ yan kungiyar sa-kai na yankin wadanda suka yi kokarin dakile aikin na su.

KU KARANTA: Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana

A wani labarin daban, Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Abubakar Gumi, ya fada a ranar Asabar cewa watakila za a sako daliban makarantar Kagara da aka sace a yau Lahadi, ganin yadda tattaunawa ke gudana tsakanin gwamnati da 'yan fashin.

Malamin, wanda ke iya shiga dazuka domin tattaunawa, nasiha da wa'azi ga manyan 'yan bindigan da yaransu, ya shaidawa manema labarai yiyuwar sakin daliban da ma'aikatan makarantar a jiya Asabar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel