Shugaba Buhari ya gargadi masu tada rikicin addini a jihar Gombe

Shugaba Buhari ya gargadi masu tada rikicin addini a jihar Gombe

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yay yi Allah wadai da rikicin sarautar Billiri a Gombe

- Shugaban ya kirayi mutanen yankin da su mayar da hankali kada su bari rikicin ya girma

- Hakazalika ya neme su da su bibiyi tarihin zaman lafiya tsakaninsu da ya hau shekearu da dama

Shugaban kasa, Manjo janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a ranar Lahadin da ta gabata ya yi nadamar cewa ’yan Najeriya sun zubar da jini sosai kan batutuwan da za a iya warware su cikin lumana.

A cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shugaban ya yi magana yayin da yake mayar da martani game da rikice-rikicen da ke faruwa a jihar Gombe wanda ya samo asali daga rikicin basaraken Billiri.

Sanarwar an yi mata taken, ‘Fadan shugabanci na Billiri: Shugaba Buhari ya la’anci tashin hankali, ya yi kira da a kiyaye sosai don kaucewa ci gaban rikicin’.

KU KARANTA: Saura kwanaki 10 allurar rigakafin Korona ta iso Najeriya, Ministan Lafiya

Shugaba Buhari ya gargadi masu tada rikicin addini a jihar Gombe
Shugaba Buhari ya gargadi masu tada rikicin addini a jihar Gombe Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shehu ya nakalto shugaban yana bayyana "babban kaduwa da damuwa matuka" kan lamarin.

Shugaban ya ce, “Na damu matuka da barkewar rikici a Jihar Gombe kuma ina kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi taka tsantsan don kauce wa ci gaban rikicin.

“Saukin warware tashin hankalin ne ba a neme shi ba saboda akwai hanyoyin da za a iya warware sabani cikin ruwan sanyi ba tare da yin barazana ga doka da oda ba.

“A cikin da’irar tashin hankali, babu masu nasara, sai masu hasara. Musulmi da Kirista ya kamata su guji fitinar shiga tashin hankali don nuna bacin ransu.

“‘ Yan Nijeriya sun zubar da isasshen jini kan batutuwan da za a iya warware su cikin lumana.

"Ina kira ga bangarorin biyu da su maida takubbansu domin a zauna lafiya. Gombe ta daɗe tana jin daɗin jituwa ta addini a cikin shekaru da yawa kuma bai kamata ku bari wasu 'yan iska su lalata wannan kyakkyawan tarihin ba."

KU KARANTA: Ku biya harajinku idan kuna son Abuja ta koma kamar Dubai, Hukumar Haraji

A wani labarin, Rikicin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyi suka yi ne wadanda ke zargin gwamnatin da rashin adalci a tsarin zaben sabon Mai Tangale a Billiri.

Hakanan akwai rikicin addini yayin da aka kona wuraren bautar musulmai a yankin na Billiri.

Amma a wani labarin, Inuwa Yahaya, gwamnan jihar, ya ce tsarin nadin sabon basaraken ya kasance a bayyane, kuma tashin hankalin ya faru ne daga wadanda ke son shafa wa gwamnati bakin fenti don ta zabi wani dan takararsu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel