Ku biya harajinku idan kuna son Abuja ta koma kamar Dubai, Hukumar Haraji

Ku biya harajinku idan kuna son Abuja ta koma kamar Dubai, Hukumar Haraji

- Hukumar haraji a babban birnin tarayya ta bukaci mazauna garin da su biya harajinsu

- Hukumar ta bayyana muhimmancin biyan harajin duba da bukatar ci gaban birnin na Abuja

- Hakazalika hukumar ta fidda wa'adi ga mazaunan domin su yi kokarin biyan harajinsu

Hukumar Kula da Haraji ta Babban Birnin Tarayya (FCT-IRS) ta bukaci duk masu biyan haraji a cikin babban birnin kasar da su gabatar da bayanan harajinsu na shekara-shekara, tana mai cewa wannan ita ce kadai hanyar da za ta sanya garin zama kamar Dubai ko Singapore.

Dubai ce kan gaba wajen yawan yawon bude ido a duniya, a rahoton Daily Trust.

A lokacin da yake zantawa da NAN a Abuja a ranar Lahadi, Abdullahi Attah, Shugaban hukumar, ya ce,

“Abuja babban birni ne, mai girman, kai kuma mai tsada wajen kula da shi, hanya guda daya tilo da za mu iya ci gaba da kiyaye Abuja daga burinmu ita ce ta hanyar biyan haraji., domin mu zama kamar Singapore da Dubai na wannan duniyar. ”

KU KARANTA: Bana son annobar Covid-19 ta kare, saboda a lokacinta na sayi jirgi na 3, in ji Fasto

Ku biya harajinku idan kuna son Abuja ta koma kamar Dubai, Hukumar Haraji
Ku biya harajinku idan kuna son Abuja ta koma kamar Dubai, Hukumar Haraji Hoto: Medium
Source: UGC

Ya ba da 31 ga Maris a matsayin wa'adi ga duk masu biyan haraji a cikin birnin su gabatar da bayanan harajinsu na shekara-shekara.

Attah ya ce doka ta bukaci duk wani mutum da ke biyan haraji da ya gabatar da rahoton karbar haraji a cikin kwanaki 90 bayan karshen shekarar kudi.

“Mun kammala shiri don aikawa da sako ta waya (SMS) ga duk masu biyan haraji a cikin bayanan mu na neman su gabatar da rahoton harajin su na shekara.
"Ina kira ga dukkan mazauna Abuja wadanda ke biyan haraji da su yi aikin da ya rataya a wuyansu kuma ina farin cikin bayyana cewa a matakin koli, manyan jami'an gwamnati sun fara yin rajistar kafin ranar 31 ga watan Maris," in ji shi.

Ya ce hukumar za ta ci gaba da wayar da kan ‘yan yankin kan mahimmancin biyan haraji, yana mai bayyana haraji a matsayin hanya mafi inganci da za ta tabbatar da ci gaba cikin sauri.

Attah, duk da haka, ya sake jaddada aniyarsa da jajircewa tare da tawagarsa masu kula da ci gaba da inganta samar da kudaden shiga a yankin.

KU KARANTA: Babu hujjar kimiyya mai nuna ganyen Bay da Kanunfari na maganin ciwon gabbai

A wani labarin, Kwamitin kwararru na kula da COVID-19 na jihar Kano, ya bullo da wani shiri na kula dada gida don kai wa ga mutane a yankuna masu nisa, a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar.

Wata sanarwa daga hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar wanda jami’in yada labaran ta Mista Maikudi Marafa ya sanya hannu, ta bayyana hakan ne a ranar Asabar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel