Saura kwanaki 10 allurar rigakafin Korona ta iso Najeriya, Ministan Lafiya

Saura kwanaki 10 allurar rigakafin Korona ta iso Najeriya, Ministan Lafiya

- Ministan lafiya ya bayyana cewa ana sa ran isaowar rigakafin Korona nan da kwana 10

- Ministan ya bayyana hakane ga manema lanbarai a jihar Legas wata ziyara da ya kai asibiti

- Ministan ya kuma bayyana yadda wasu kasashe tuni suka fara kaddamar da allurar rigakafin

Ministan lafiya Osagie Ehanire ya fada a Lagas jiya cewa Najeriya na iya samun allurar rigakafin COVID-19 nan da kwanaki 10 masu zuwa, The Nation ta ruwaito.

Ministan ya ce "An gaya mana cewa a karshen wannan watan, wato kimanin kwanaki 10 kenan daga yanzu, za mu sami alluran."

“Ba mu kera alluran ba. Ana kera su ne a kasashen waje a cikin kasashe kamar hudu ko biyar," kamar ydda ya fada wa manema labarai a karshen ziyarar rangadin asibitin koyarwa na jami'ar Legas (LUTH), Idi-Araba.

Ehanire ya bayyana cewa Amurka, Ingila, Rasha da China da suka yi nasarar samar da alluran rigakafin yanzu suna ba wasu lasisin sake yin su.

KU KARANTA: NALDA zata tallafawa masu kiwon kifi 2,000 a jihar Borno da wasu 1,040

Saura kwanaki 10 allurar rigakafin Korona ta iso Najeriya, Ministan Lafiya
Saura kwanaki 10 allurar rigakafin Korona ta iso Najeriya, Ministan Lafiya Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ministan ya ce "Afirka ta Kudu na da lasisin yin allurar rigakafin Johnson & Johnson COVID-19, yayin da a kwanan nan Rasha ta bai wa Indiya lasisin samar da AstraZeneca."

Ya ce kasashen da suka samar da alluran suna da manyan kalubale tare da COVID-19 kuma sun yanke shawarar halartar bukatunsu da farko, yanayin da WHO ta bayyana hakan a matsayin kishin kasa na allurar rigakafi.

Ehanire ya lura cewa yayin da duk duniya ke fama da cutar ta COVID-19, ana amfani da kusan kashi 75 na allurar rigakafin da aka riga aka samar ana amfani da su a ƙasashe 10.

Ministan ya jaddada cewa Najeriya ta sanya dukkan kayan aiki a wurin domin karbar alluran rigakafin.

Da yake maraba da Ministan tun da farko, Babban Daraktan Likitanci na LUTH, Farfesa Chris Bode, ya nemi Ministan ya taimaka a wajen daukar ma’aikatan jinya 350, masu ba da shawara 50 da jami’an lafiya 150.

Farfesa Bode ya ce asibitin ya kuma bukaci samar da iskar Oxygen tare da kara yawan kudade don gina cibiyar kebewa mai hawa hudu, gudanar da asibitin yadda ya kamata da kuma biyan makuddan kudade na wutar lantarki kowane wata.

KU KARANTA: 2023: Jerin manyan arewa dake goyon bayan mayar da mulkin Najeriya Kudu

A wani labarin, Kwamitin kwararru na kula da COVID-19 na jihar Kano, ya bullo da wani shiri na kula dada gida don kai wa ga mutane a yankuna masu nisa, a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar.

Wata sanarwa daga hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar wanda jami’in yada labaran ta Mista Maikudi Marafa ya sanya hannu, ta bayyana hakan ne a ranar Asabar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel