Mun sa an saki mutane fiye da 1,000 da aka sace ba tare da kudin fansa ba, Matawalle

Mun sa an saki mutane fiye da 1,000 da aka sace ba tare da kudin fansa ba, Matawalle

- An saki kimanin mutane 1000 da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan ko sisi ba, Gwamna Matawalle ya bayyana

- Hakazalika, yan bindiga sun mika manyan makamai fiye da 300 a jihar

- A cewar gwamnan, a shirye yake ya yi duk abin da zai sa a zauna lafiya a Zamfara

A wani labari da zai jawo martani daban-daban daga 'yan Najeriya, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi rawar gani wajen ganin an sako wadanda aka yi garkuwa da su.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta tabbatar da sakin sama da mutane 1,000 daga masu satar mutane.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun saki Okorocha yayin da gwamnoni suka shiga tsakani a fadarsa da Uzodinma

Mun sa an saki mutane fiye da 1,000 da aka sace ba tare da kudin fansa ba, Matawalle
Mun sa an saki mutane fiye da 1,000 da aka sace ba tare da kudin fansa ba, Matawalle Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Matawalle wanda ya bayyana hakan a gidan Talabijin na Channels ya ce an saki mutanen ba tare da biyan kudin fansa ba.

Ya ce: “Mun kuma sa an saki mutane 1,000 da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan kudin fansa ba. Haka kuma mun amshi manyan makamai sama da 300 wadanda barayi da shugabanninsu suka sallama.”

Da yake ci gaba da magana, ya ce zai yi duk abin da zai sa jihar Zamfara ta zauna lafiya. Ya kuma bayar da hujjar cewa tattaunawa tare da 'yan fashi da masu laifi zai sa kasar ta zauna lafiya.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayin da hotunan kyawawan jami’an da suka mutu a hatsarin jirgin saman Abuja ya bayyana

Ya kara da cewa:

A ganina, a matsayina na jagora, ba zan iya nade hannuwana ina kallo ana kashe mutanena kowace rana. Dole ne in fara duk wani abu da na san zan iya sanya jama’ata su yi bacci idanunsu biyu, in ji gwamnan wanda ya yi kwamishina a jihar tsakanin 1999 da 2003.

“Wannan shine dalilin da yasa dole na fara wannan tattaunawar da mutanen nan. Kuma na yi imanin cewa zuwa lokacin da dukkan gwamnoni za su hadu su amince a kan yin hakan, za mu iya samar da tsaro a kasarmu."

A gefe guda, wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da Alhaji Ibrahim Ahmed mai shekaru 91.

Dattijon shine dagacin kauyen Kunduru da ke karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina.

Wani mazaunin yankin ya ce an sace dagacin ne a daren Juma'a yayin da 'yan bindiga suka tsinkayi gidan basaraken da ke Kunduru kuma suka yi awon gaba da shi.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel