'Yan bindiga sun yi awon gaba da dagaci a jihar Katsina

'Yan bindiga sun yi awon gaba da dagaci a jihar Katsina

- Miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da Alhaji Ibrahim Ahmed mai shekaru 91

- Tsohon shine dagacin kauyen Kunduru da ke karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina

- Sun sace mahaifin babban sakataren gwamnatin jihar Katsina, Kashimu Ibrahim ranar Juma'a

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da Alhaji Ibrahim Ahmed mai shekaru 91.

Dattijon shine dagacin kauyen Kunduru da ke karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina.

Wani mazaunin yankin ya ce an sace dagacin ne a daren Juma'a yayin da 'yan bindiga suka tsinkayi gidan basaraken da ke Kunduru kuma suka yi awon gaba da shi.

KU KARANTA: Saboda mata: ISWAP da bangaren Shekau anyi artabu, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa

'Yan bindiga sun yi awon gaba da dagaci a jihar Katsina
'Yan bindiga sun yi awon gaba da dagaci a jihar Katsina. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar tace, wanda aka sace din shine mahaifin Kashimu Ibrahim, daya daga cikin manyan sakatarorin gwamnatin jihar Katsina.

Amma kuma, daya daga cikin 'ya'yan basaraken ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a garin Katsina, Leadership ta tabbatar.

Dan basaraken wanda ya bukaci a adana sunansa ya ce 'yan bindiga sun shiga kauyensu a kan babura inda suka kai musu hari.

KU KARANTA: Jerin sunayen dakarun sojin sama da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama

A wani labari na daban, ashe sojojin sama na NAF201 da suka yi hatsari a jirgin sama, har mutane 7 da matukan jirgi da suka mutu a Abuja, suna neman wadanda aka sace a Kagara ne, kamar yadda bayanai suka bayyana a ranar Lahadi da yamma.

Kamar yadda aka samu labari, bayan kara wa jirgin mai a Abuja, jirgin ya bazama neman 'yan makarantan Kagara da aka sace ne a jihar Neja, Vanguard ta wallafa.

"Jirgin ya nufi Abuja don shan mai, injin jirgin ya samu matsala yayin da ya keta hazo ya kasa sakkowa duk da kokarin da yayi don sauka lafiya."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel