Hawaye sun kwaranya yayin da hotunan kyawawan jami’an da suka mutu a hatsarin jirgin saman Abuja ya bayyana
- Ana ci gaba da yin martani kan hatsarin jirgin saman da ya kashe wasu hafsoshin Sojan Sama na Najeriya
- Abokan Laftanal Haruna Gadzama sun bayyana kyawawan halayensa
- Tuni rundunar sojin saman Najeriya ta fara bincike kan musabbabin hatsarin
Abokan wani matukin jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya (NAF) B350i da ya yi hatsari a Abuja na jimamin mutuwar abokin aikinsu.
Mahukunta sun bayyana cewa Laftanal Haruna Gadzama daga jihar Borno na daya daga cikin matukan jirgin da suka yi hatsarin.
Abokan karatunsa daga makarantar Sakandaren Sojan Sama da ke Kaduna sun aike da sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin.
KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da dagaci a jihar Katsina
Abokan aikin nasa a karkashin kungiyar, tsoffin kananan matukan jirgi, a wani sako da suka wallafa a shafin Facebook, sun bayyana shi a matsayin jami'in rundunar sojin sama mai aiki tukuru wanda za a yi kewa.
Sakon ya ce:
`` Muna bakin cikin mutuwar Flt Lt CH Gadzama na rukunin 07 a Makarantar Sakandaren Sojojin Sama da ke Kaduna a ranar Lahadi 21 ga watan Febuary 2021. Ya kasance mutum mai fara'a kuma jami'in rundunar Sojin Sama mai jajircewa a kan aiki.
Muna mika t'aaziyarmu a kan rashin Membobinmu, da yawa daga cikinmu mun san shi kuma halayensa abun so ne, Za a yi kewarsa. A madadin kungiyar tsoffin kananan matukan jirgi (EX-JPs), Muna miƙa ta'aziyyarmu ga NAF da Iyalansa a wannan lokacin na alhini. Allah ya sa ya huta."
Hakazalika, wata mai amfani da shafin Twitter, Lem Wamdeo, ta ce matukin jirgin dan uwanta ne, inda ta bayyana hatsarin a matsayin abin bakin ciki.
KU KARANTA KUMA: Masu adaidaita-sahu a Kano sun tsinduma yajin aiki saboda harajin N100
Har ila yau, wata hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie ma ta jinjina wa jami’an da suka mutu a hatsarin.
Onochie a wani sako da ta wallafa a shafin Twitter ta buga hoton wasu daga cikin jami’an da suka rasa rayukansu a lamarin.
Ta gode musu kan hidimar da suka yi wa kasa sannan kuma ta tausaya wa danginsu game da wannan abun bakin ciki da ya faru.
A gefe guda, mun ji cewa ashe sojojin sama na NAF201 da suka yi hatsari a jirgin sama, har mutane 7 da matukan jirgi da suka mutu a Abuja, suna neman wadanda aka sace a Kagara ne, kamar yadda bayanai suka bayyana a ranar Lahadi da yamma.
Kamar yadda aka samu labari, bayan kara wa jirgin mai a Abuja, jirgin ya bazama neman 'yan makarantan Kagara da aka sace ne a jihar Neja, Vanguard ta wallafa.
"Jirgin ya nufi Abuja don shan mai, injin jirgin ya samu matsala yayin da ya keta hazo ya kasa sakkowa duk da kokarin da yayi don sauka lafiya."
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng