'Yan sanda sun saki Okorocha yayin da gwamnoni suka shiga tsakani a fadarsa da Uzodinma

'Yan sanda sun saki Okorocha yayin da gwamnoni suka shiga tsakani a fadarsa da Uzodinma

- Rundunar yan sandan Najeriya ta saki sanata Rochas Okorocha bayan tsare shi na dan lokaci

- Hakan ya biyo bayan takkadamar da ke tsakaninsa da magajinsa, Gwamn Hope Uzodinma na jihar imo

- Tuni dai kungiyar gwamnonin kudu ta shiga tsakani domin yi masu sulhu

Kungiyar Gwamnonin Kudu Maso Gabas ta ce ta sanya baki a takun-sakar da ke tsakanin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da magajin sa, Hope Uzodinma.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ‘yan sanda a ranar Lahadi sun cafke Mista Okorocha a yayin da ake takaddama kan yadda gwamnati ta rufe wani otal, Royal Spring Palm Hotel, na matarsa.

An saki Mista Okorocha wanda ya kasance dan majalisar dattawa mai ci daga hedkwatar ‘yan sanda, Owerri, inda aka tsare shi na wani dan lokaci sannan kuma aka nemi ya mayar da martani kan korafin da Gwamnatin Jihar Imo ta shigar a kansa.

'Yan sanda sun saki Okorocha yayin da gwamnoni suka shiga tsakani a fadarsa da Uzodinma
'Yan sanda sun saki Okorocha yayin da gwamnoni suka shiga tsakani a fadarsa da Uzodinma Hoto: @PremiumTimesng
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayin da hotunan kyawawan jami’an da suka mutu a hatsarin jirgin saman Abuja ya bayyana

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Ikeokwu Orlando, da mai taimaka wa Sanata Okorocha, Ebere Nzewuji, sun tabbatar wa majiyarmu ta Premium Times cewa an saki sanatan a daren Lahadi.

Shugaban kungiyar, David Umahi, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Francis Nwaze, a ranar Litinin, ya ce kungiyar ta "riga ta shiga lamarin" da ke tsakanin Sanata Okorocha da Gwamna Uzodinma.

Mista Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya ce tuni an tuntubi wadanda za su sasanta rikicin sannan ya bayar da tabbacin cewa dukkan bangarorin sun amince da sulhu.

Mista Umahi ya bukaci mazauna Imo da su gudanar da kasuwancinsu cikin lumana da bin doka.

Gwamnan ya kara da cewa

"Ya kamata su kuma guji kalaman tunzurawa yayin da muke aiki don maido da zaman lafiya yadda aka saba."

Tun lokacin da ya bar ofis a matsayin gwamna a shekarar 2019, Mista Okorocha ke ta fama da rikicin siyasa tare da wanda ya gaje shi, Mista Uzodinma.

Dukkansu su biyun ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne a Najeriya.

Hadimin Okorocha, Mista Nzewuji, a ranar Lahadi, ya ce rikicin da ke tsakanin sanatan da Mista Uzodinma ba komai bace face mayyar farauta ta siyasa da magajin nasa ke masa.

“Wannan duk lamarin siyasa ne wanda baya rasa nasaba da zaben shugaban kasa na 2023.

"Ana ganin Sanata Okorocha a matsayin tauraron da zai fi kowanne haskawa daga wannan yanki na kasar, kuma wasu mutane a wajen yankin suna amfani da 'yan uwansa da ke wurin don kunyata shi," in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya rasuwa a Kwara

Mista Nzewuji ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin siyasa a kasar nan da su shiga tsakani a rikicin Okorocha da Uzodinma.

A wani labarin, Basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel