Har yanzu ba’a sako ɗalibai da malaman makarantar GSS Kagara ba

Har yanzu ba’a sako ɗalibai da malaman makarantar GSS Kagara ba

- Dalibai da malaman kwallejin kimiyya na gwamnati da ke Kagara da yan bindiga suka sace har yanzu suna hannunsu

- Sakatariyar watsa labarai na gwamnan jihar Niger, Mary Noel-Berje ta tabbatar da hakan

- Mary Noel-Berje ta ce wadanda aka sako fasinjojin NSTA ne da aka yi garkuwa da su ba yan makarantar Kagara ba

A wani taron manema labarai a Minna, babban birnin jihar, a daren Lahadi, gwamnan ya ce ana kokarin kubutar da su ba tare da rauni ba.

Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya ce ba a saki wadanda aka sace a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a jihar Neja ba.

Da farko mun kawo muku cewa an sako mutane 42 da yan bindiga suka sace daga kwallejin kimiyya na gwamnati da ke Kagara a jihar Niger, bisa rahoton The Nation.

Har yanzu ba’a sako ɗalibai da malaman makarantar GSS Kagara ba
Har yanzu ba’a sako ɗalibai da malaman makarantar GSS Kagara ba. Hoto: Premium Times
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Bayan budurwarsa ta haifa ma sa ɗa, sai ya gudu ya bar gari tare da surukuwarsa

Wadanda aka sace sun hada da dalibai 27, ma'aikata 3 da kuma iyalan ma'aikatan su 12.

Majiyoyi sun ce wadanda aka sace din suna kan hanyarsu na komawa Minna a yanzu.

KU KARANTA: Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel