Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana

Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana

- Rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa ya lafa kasuwar Sasha bayan daukar kwanaki ana yi

- Shaidun gani da ido da gidajen jaridu sun bayyana ainihin yadda lamarin ya faru a kwanakin

- Legit.ng Hausa, mun tattaro muku labarin yadda lamarin ya faru da kuma halin da ake ciki

Bayan fada tsakanin Yarbawa da Hausawa a kasuwar Shasha da ke Ibadan, asarar ta ratsa kabilun biyu; hatta shugabanni a cikin al'umma sun yi asarar da ta wuce lissafi.

Amma mako guda bayan mulkin tashin hankalin, kabilun biyu sun taru a karkashin rufi daya don yin sallar jam'i ta Juma'a aranar Juma'a.

Rashidi Muraina, babban limamin da ya jagoranci sallar a babban masallacin kasuwar Shasha, ya shaida wa TheCable cewa da an kauce wa rikicin idan da wadanda abin ya shafa sun yi hakuri.

KU KARANTA: Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa

Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana
Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana Hoto: ThCable
Asali: UGC

Ya sake bayar da labarin: “Sun ce wani bahaushe ne, wanda ke tura amalanke, ya zubar da tumatir a gaban shagon wata mata mai ciki.

"Ya kuma lakadawa mai cikin duka lokacin da ta kawo kara. Sannan wani mutum, mai gyaran takalmi, ya kalubalanci bahaushen da ya daina dukar matar mai ciki.

“Daga nan sai bahaushen ya bugi mai gyaran takamin. Mutumin ya mutu bayan ‘yan sa’o’i a Asibitin. Shugaban hausawan ya nemi su kawo wanda ya kashe su kuma su biya N30,000 da aka ajiye a asibiti kafin mai gyaran takalmin ya mutu.

“Washegari da safe, wasu mutane sun taru a shagon marigayin domin yi masa makoki amma wasu matasan Hausawa suka far musu, lamarin da ya haifar da rikici mai yawa.

"Daruruwan gidaje da shaguna sun kone yayin da kayayyakin abinci na miliyoyin nairori suka lalace. Wannan shine kawai abin da muka sani game da rikicin. Wadannan Hausawan suna zaune a tsakaninmu; wasunsu suna kwana a kasuwa.

“Dan uwana ya mutu cikin tashin hankalin. Na gudu daga gidana sai daya baya na dawo; 'yan kwanakin baya. An kone babban masallacin.”

Babban limamin da yake bin diddigin asalin bambance-bambancen da ke tsakanin kabilun biyu a yankin, ya ce takaddama a kan wanda zai zama shugaban kasuwar Shasha ya haifar da tashin hankali a tsakanin 'yan kasuwa a kasuwar.

A cewarsa, shugaban al'ummar Hausawan ya kasance yana goyon bayan wani shugaban Yarbawa amma 'yan uwansa suna adawa da ra'ayin.

“Seriki Shasha, shugaban al’ummar Hausawa, na goyon bayan zabar wani Bayarabe a matsayin shugaban kasuwar.

"Ya fada wa mutanensa cewa filin na Yarabawa ne kuma su ne masu masaukin. Amma mutanensa sun saba da ra'ayinshi; ba sa son Bayarabe ya zama shugaban kasuwa. Wannan rikicin shine dalilin da yasa bamu da shugaban kasuwa," ya kara da cewa.

Muraina ya bayyana cewa ana zaman lafiya a sarautar kasuwar har sai da batun shugabancin kasuwar ya gurbata daga baya. Sai dai ya ce duk da rikicin, kabilun biyu sun taru don yin sallar Juma'a a masallacin da suka kona da farko.

“A lokacin sallar Juma'a, dubban mutane, Yarbawa da Hausawa sun taru a wurin don yin sallah.

"Muna zaune lafiya sai dai rikicin shugabancin kasuwa. A ranar Juma'a, mako guda bayan fadan, adadin ya ragu amma duka al'ummomin Yarbawa da Hausawa sun manta bambance-bambancen da ke tsakaninsu don yin sallar Juma'a a masallacin da aka kona.

“Mun gaisa da junanmu kuma mun yi musayar abubuwa masu dadi. Akwai mazajen hausa da yawa wadanda suke auren da yaranmu mata. Matsalar ta wuce duk da ciwo da asara,” in ji Murania.

KU KARANTA: Gamayyar gwamnoni tayi alkawarin tallafawa Makinde a sake gina kasuwar Sasha

Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana
Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana Hoto: TheCable
Asali: UGC

An nada Bayarabe shugaban kasuwar Sasha

A gidan Hamza Akinade, Baale na garin Shasha, sarakunan gargajiya, mutanen da suka rasa muhallinsu, da matasa sun hallara don tausaya masa. 'Yan sanda da aka girke a bakin titi, inda fadar Baale ta ke, sun ki ba motocin damar shiga.

Baale ya fadawa manema labarai cewa zaman lafiya ya dawo cikin jama’arsa, yana kira ga Hausawan da suka gudu da su koma kasuwa. Ya kuma godewa gwamnonin da suka ziyarta tare da alkawarin sake gina kasuwar da gidajen da aka kona.

“Gwamnoni daga jihohin Arewa da na Oyo sun zo sun yi alkawura. Sun ce zasu zo su sake gina shagunan. Sun kuma ba wasu 'yan kasuwan kayan taimako.

"Idan ka shiga kasuwar da ta kone, za ka gansu suna tattara kayan cikin dandazo. Muna kira ga Hausawa da suka gudu su komo Shasha, babu sauran fada. Mu ‘yan uwan juna ne,” in ji shugaban jama’ar.

Da aka tambaye shi ko al’ummar ba za su zauna a kan tsanar juna duba da hargitsin shugabanci a kasuwar da har yanzu ba a warware su ba, sai Baale ya ce ya hadu da Seriki Shasha kuma an zabi wani Bayarabe ya jagoranci kasuwar.

“Batun shugabancin kasuwa an daidaita. Na yi magana da Seriki Shasha, shi ya samar da mataimakin shugaban kasuwar sannan ni kuma na samar da shugaban wanda Yarabawa ne.

"Har yanzu bamu gama rantsar dasu ba. Babu sauran fada a kan batun. Gwamnan jihar da kakakin majalisar dokokin suna goyon baya,” in ji Baale.

'Yan kasuwa sun tafka asara

Alarape Isiaka wata mai sayar da buhunan kayan abinci a kasuwar. Ta cika shagon da sabbin kayayyaki kwana daya kafin rikicin. Mutum ba zai yarda ba cewa shago cike da kaya shine a sararin da ta nuna a matsayin shagonta ba.

Abin da ya rage lokacin da manema labarai suka ziyarta ziyarta a ranar Asabar toka ce. A cewar ta, ta yi asarar Naira miliyan 4 a rikicin.

Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana
Rikicin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha: Me ya faru kuma a ina aka kwana Hoto: TheCable
Asali: UGC

Ta ce: “Ina siyar da kayan sari ne. Na kasance ina kasuwa anan shekaru 35 da suka gabata amma fatana ya dogara ga taimako daga Allah da kuma gwamnati.

"Ni bazawara ce, na cika shago kwana daya kafin tashin hankalin amma ban siyar da komai daga ciki ba aka kone shi. Na yi asarar kusan Naira miliyan 4.

“An kai hari gidana amma mutane sun taimaka min na wutar. Muna fitowa, sai muka ga shagunan sun yi kaca-kaca. Muna hulda da Hausawa sosai a kasuwa amma wannan abin mamaki ne.”

Fatima Awawu daga Kano ta zauna a garin Shasha tsawon shekara 30. Bayan rasuwar mijinta shekaru biyar da suka gabata, wata kawar Yarbawa ta shawo kanta cewa kada ta koma arewa bayan ta kwashe shekaru da yawa a garin na Ibadan.

Tana daya daga cikin 'yan kasuwar Shasha wadanda suka rasa duk abin da suke da shi.

“Bayan na idar da Sallah a safiyar wannan rana, sai na wuce zuwa shago na amma ban samu damar isa shagon ba saboda rikici ya barke kuma kowa na gudun tsira.

“Na nemi mafaka a wani wuri ina hangowa daga nesa yayin da shago na ya lalace. Ni bazawara shekara biyar. da mutuwar mijina.

"Ina da wata kawata Bayarbiya wanda ta tallafa mini don fara kasuwa bayan mutuwar mijina. Ita ce ta ja hankalina na kada na koma Kano. Yanzu, ba ni da komai, maharan sun kone shagunan mu.”

A wani labarin, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnoni hudu daga yankin arewacin Najeriya a yanzu haka suna ganawa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Taron ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabanin Fulani, manoma da sarakunan gargajiya a jihar.

Farfajiyar zaman lafiyan na faruwa a Obas ’Complex, Sakatariyar Jiha, Oke Mosan, Abeokuta.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel