Gwamnatin jihar Kano ta kirkiro shirin kula da masu Korona daga gida

Gwamnatin jihar Kano ta kirkiro shirin kula da masu Korona daga gida

- Gwamnatin jihar Kano ta yi kudirin tabbatar da kawar da cutar Korona a duk fadin jihar

- Gwamnatin ta dauki ma'aikata ta kuma samar da kayanaiki don isa ga yankuna masu nisa

- Wata sanarwar gwamnatin ta bayyana shirin gwamnati na isa ga mutanen karkara a jihar

Kwamitin kwararru na kula da COVID-19 na jihar Kano, ya bullo da wani shiri na kula dada gida don kai wa ga mutane a yankuna masu nisa, a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar.

Wata sanarwa daga hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar wanda jami’in yada labaran ta Mista Maikudi Marafa ya sanya hannu, ta bayyana hakan ne a ranar Asabar.

Ya ce kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Aminu Tsanyawa, wanda ya kaddamar shirin a ranar Asabar, ya ce ya zama dole a takaita yaduwar cutar a karo na biyu.

Kwamishinan ya jaddada cewa an horas da ma’aikatan kiwon lafiya tare da basu babura da magunguna don isa da yankuna, da nufin bada kulawar gaggawa ta kiwon lafiya.

KU KARANTA: Buhari ya amince da bai wa sabbin jami’o’i 20 masu zaman kansu lasisi

Gwamnatin jihar Kano ta kirkiro shirin kula da masu Korona daga gida
Gwamnatin jihar Kano ta kirkiro shirin kula da masu Korona daga gida Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Sanarwar ta ce "Dokta Tsanyawa ya bukaci ma'aikatan lafiya da aka dora masu nauyin gudanar da aikin, don su himmatu wajen ganin an kammala aikinsu."

Bayanin ya ci gaba da bayyana cewa Kodinetan kwamiti, da kuma Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko, Dokta Tijjani Hussain, sun ce shirin zai yi amfani da samfuran da aka yi nufin yi ga al'umma.

Hussaini ya kuma bayyana cewa shirin na nufin bayar da agajin gaggawa ga mutanen da ke cikin wahalar isar da sako ga al'ummomin jihar.

Ya yaba wa gwamnatin jihar kan goyon bayan da take bai wa kwamitin rundunar, a kokarin da take yi na kawar da cutar a jihar, kamar yadda yake kunshe cikin sanarwar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa Dakta Hussaini ya yi kira ga jama’ar jihar da su bai wa ma’aikatan lafiya dukkan goyon baya da hadin kai, don cimma burin shirin.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kogi ta yi barazanar maka NCDC da PTF a kotu

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da wasu jami'ai 2,000 na COVID-19 domin fadakarwa tare da aiwatar da ladabi kan tsaro a jihar, PM News ta ruwaito.

Ganduje ya ce a lokacin kaddamarwar a Kano ranar Lahadi cewa akwai bukatar a magance COVID-19 da dukkan kokari da za a iya yi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel