Bana son annobar Covid-19 ta kare, saboda a lokacinta na sayi jirgi na 3, in ji Fasto

Bana son annobar Covid-19 ta kare, saboda a lokacinta na sayi jirgi na 3, in ji Fasto

- Wani babban malamin coci ya bayyana ra'ayinsa da cewa Korona alherine gareshi

- Faston, ya bayyana irin morar annobar Korona da yayi a yayin da kowa ke wahala

- Ya kuma sanar da sayen jirginsa na uku, wanda a lokacin Korona ya samu kudin ya siya

Babban malamin cocin Omega Fire Ministries International, Apostle Johnson Suleman, ya ce ya sayi jirginsa na uku a yayin da annobar COVID-19 ta barke wanda ya jefa kasar cikin matsin tattalin arziki.

Malamin ya ci gaba da cewa, yana addu'ar kada cutar ta kare saboda yana samun ci gaba yana kuma hutawa. Legit.ng Hausa ta gano bidiyon Faston yana jawabi kan yadda ya tara kudaden da ya sayi jirgin.

KU KARANTA: Babu hujjar kimiyya mai nuna ganyen Bay da Kanunfari na maganin ciwon gabbai

Wani Fasto yayi addu'ar kada Korona ta kare, saboda da yafi samu da Korona
Wani Fasto yayi addu'ar kada Korona ta kare, saboda da yafi samu da Korona Hoto: AkPraise
Asali: UGC

Ya ce, “A lokacin annobar COVID na sayi jirgi; na uku. Ina da uku yanzu. Ina ta addu'ar kada COVID-19 ya ƙare saboda ina hutawa. Yayin da mutane suke gunaguni, matata ta tambaya, ‘Shin rayuwa za ta iya zama mai daɗi haka?’ Shin ina magana da wani a nan?”

“Babu damuwa. Na karanta a Intanet cewa akwai jita-jita da ke yawo cewa ina da wata na'ura da take buga kuɗi. Ina son wannan jita-jita. Suna cewa, ‘ya kamata a bincike shi. Yana da injin da yake buga kudi.

“Wani ya tambaya ko gaskiya ne kuma na ce gaskiya ne. Suka ce, 'Yana da haɗari fa'. Na ce ban sani ba yana da haɗari saboda na riga na sayi injin. Lokacin da kuke magana da bakinku, kuna buga kudi ne."

KU KARANTA: EFCC: Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta yaba wa Buhari kan nadin Bawa

A wani labarin, Wani jigo a jam’iyyar PDP, kuma Shugaban kungiyar Revival na PDP, Malam Tanko Ibrahim ya caccaki tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose kan kalaman da ke cewa Idan Kayode ya bar PDP, zai mutu a siyasance.

Mallam Tanko Ibrahim ya fadi wannan bayanin ga jaridar Vanguard a ranar Talata.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.