Bayan jihar Oyo, gwamnonin Arewa sun garzaya jihar Ogun

Bayan jihar Oyo, gwamnonin Arewa sun garzaya jihar Ogun

- Gwamnonin jihohin kudu 2 sun hadu don tattaunawa da wasu gwamnonin arewa 4

- Gwamnonin sun zauna ne don tattaunawa kan matsalar rikicin Fulani makiyaya

- Gwamnonin a halin yanzu suna zaman tattaunawar, fatan a samu matsaya mai kyau

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnoni hudu daga yankin arewacin Najeriya a yanzu haka suna ganawa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Taron ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabanin Fulani, manoma da sarakunan gargajiya a jihar.

Farfajiyar zaman lafiyan na faruwa a Obas ’Complex, Sakatariyar Jiha, Oke Mosan, Abeokuta.

KU KARANTA: ‘Yan Shi’a sun nemi ayi musu adalci kan kisan gilla da aka musu a Zariya

Abiodun da Akeredolu sun gana da gwamnonin Arewa 4 kan rikicin Manoma/Makiyaya#
Hoto: The Sources NG
Abiodun da Akeredolu sun gana da gwamnonin Arewa 4 kan rikicin Manoma/Makiyaya
Asali: UGC

Gwamnoni daga arewa wadanda suke zaman sune; Bello Matawale (Zamfara), Atiku Bagudu (Kebbi), Abdullahi Ganduje (Kano) da Gwamnan Neja, Abubakar Sanni Bello.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankunan da ake rikici a Yewaland ya lakume rayukan mutane akalla goma a cikin mako guda da ya gabata.

Wasu daga cikin yankunan da fulani makiyaya suka far wa; Eggua, Ketu, Igbooro, Iselu, Agbon-Ojodu, Asa, Ibeku, Imeko da Oja-Odan.

Abiodun, a ranar Litinin da yamma, jim kadan bayan kammala wani taron gudun fanfalaki da shugabannin hukumomin tsaro a jihar, ya nufi yankunan da ake rikici yayin tashin hankali.

Daga baya ya ziyarci Igbooro inda aka kashe mutane uku kuma tara suka ji rauni a harin daren Lahadi.

Gwamnan, yayin da yake magana game da taron masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewa ya gayyaci gwamnonin arewa biyar wadanda suka fito daga Fulanin da za su halarci taron a ranar Talata.

KU KARANTA: An yanke wa wanda ya kashe jami'in Jumia hukuncin kisa ta hanyar rataya

A wani labarin, Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya (NYCN) ta nuna damuwarta kan yawan hare-haren da ake zargin ‘yan Arewa da kai wa, musamman harin baya-bayan nan a kasuwar Sasha ta karamar Hukumar Akinyele da ke Oyo, The Nation ta ruwaito.

Wata sanarwa daga kakakinta, Mock Kure, ta ce: “Hankalin Majalisar Matasan Arewacin Najeriya ya karkata ne kan barna da ake yi wa 'yan Arewa, musamman a Kasuwar Sasha ta Karamar Hukumar Akinyele, Jihar Oyo, Kudu maso Yammacin Najeriya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel