Gamayyar gwamnoni tayi alkawarin tallafawa Makinde a sake gina kasuwar Sasha

Gamayyar gwamnoni tayi alkawarin tallafawa Makinde a sake gina kasuwar Sasha

- Kungiyar gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa zasu tallafa wajen sake gina Sasha

- Kungiyar ta bayyana haka ne a kokarinta na shawo kan rikicin da ya faru a jihar Oyo a makon

- Hakazalika kungiyar ta gargadi al'umomin yankin da su bi doka da oda don wanzan da zaman lafiya

A matsayin wata hanya ta tabbatar da farfadowar tattalin arziki cikin sauri ga yan kasuwa da mazauna al'ummomin Shasha, kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) sun bayyana shirinsu na goyon baya ga gwamna Seyi Makinde don sake gina kasuwar Sasha.

Kungiyar wacce ta ce tuni ta bai wa wasu wadanda abin ya shafa taimako, ta kuma yi kira ga dukkan masu fada a ji a shafukan sada zumunta da su yi taka tsan-tsan don kar a rura wutar rikici a cikin rahoton nasu, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: 'Yan bindiga na neman N10m kudin fansar 'yan uwan ango da amarya da aka sace

Gamayyar gwamnoni tayi alkawarin tallafawa Makinde a sake gina kasuwar Sasha
Gamayyar gwamnoni tayi alkawarin tallafawa Makinde a sake gina kasuwar Sasha Hoto" Premium Times
Source: UGC

Gwamnan Kebbi Abubakar Bagudu ya bayar da wannan tabbacin a ranar Talata yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Ofishin Gwamnan Oyo, Agodi, Ibadan jim kadan bayan dawowa daga rangadin Shasha inda suka gana da wadanda abun ya shafa.

Gwamnan na Kebbi ya ce tawagar ta yi farin ciki da abin da suka gani a kasa don dakile ikirarin firgici, fargaba da kuma haifar da rikicin kabilanci a jihar.

Ya yi kira ga wadanda ke jin tsoron fargabar ci gaba da kai hare-hare na mazauna da su kai rahoton hakan a gidan Gwamnati don kuwa Gwamnan zai iya tura tawaga don tabbatar da magance duk wani tashin hankali.

“Abubuwan da zasu faru zasu faru, wani lokacin, wasu bata gari ne ke amfani da su don sata da haifar da tashin hankali kuma wani bangare na abin da ya faru a Ibadan yana da nasaba da hakan, kamar dai yadda muka gani yayin rikicin EndSars.

"Amma, muna farin ciki cewa dalili yana kan gaba kuma mutane suna kwantar da hankali da ƙarfafa wasu. in ji shi.

KU KARANTA: EFCC: Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta yaba wa Buhari kan nadin Bawa

A wani labarin, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnoni hudu daga yankin arewacin Najeriya a yanzu haka suna ganawa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Taron ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabanin Fulani, manoma da sarakunan gargajiya a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel