Ba da jimawa ba za a saki daliban Kagara da aka sace, in ji shugaban ‘yan fashin Zamfara

Ba da jimawa ba za a saki daliban Kagara da aka sace, in ji shugaban ‘yan fashin Zamfara

- Nan ba da jimawa ba za a saki daliban Kagara da aka sace a cewar Dogo Gide

- Shugaban ‘yan fashin ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da jami’an gwamnatin jihar Neja

- Sai dai kuma, ya bayyana cewa wadanda aka sace ba sa cikin sansanin sa

Wani babban dan bindiga a jihar Zamfara ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a saki malamai da daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara da aka sace a jihar Neja.

Dan fashin, Dogo Gide, wanda ke jar ragamar kula da dajin kudancin Zamfara ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da jami'an gwamnatin jihar Neja, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger

A cewarsa, duk da cewa wadanda aka sacen ba su a sansaninsa, zai tattauna da sauran 'yan ta'addan don hanzarta sakinsu.

Ba da jimawa ba za a saki daliban Kagara da aka sace, in ji shugaban ‘yan fashin Zamfara
Ba da jimawa ba za a saki daliban Kagara da aka sace, in ji shugaban ‘yan fashin Zamfara Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya ce:

"Imma a ce 'yan fashi sun sace mutanen ne a cikin jihar Zamfara ko kuma wasu jihohin da ke makwabtaka da Neja, Kebbi da Kaduna za a sake su nan ba da jimawa ba."

Da yake magana a kan dalilin da ya sa 'yan ta'adda suka mamaye wurin, ya yi ikirarin cewa an bar Fulani ba su da wani zabi da ya wuce su dauki makamai sannan kuma su shiga kungiyar' yan ta'adda saboda hare-hare da kashe-kashe da kungiyoyin 'yan banga da Yan-sakai suka yi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe makiyayi da direban roka a Kaduna, in ji Kwamishina

A gefe guda, a ranar Alhamis, har an fara sa ran sako dalibai da malaman makarantar GSC Kagara da aka sace, amma aka samu cikas saboda yan bindigan sun tsaya kan bakansu cewa sai an biya kudin fansa N500 million.

Sun bukaci wannan kudi ne matsayin kudin fansan matafiyan motar NSTA da suka sace, da kuma mutane 42 na makarantar GSC Kagara, Thisday ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, wanda ke cikin mutanen da ke tattaunawa da yan bindigan ya ce sun bukaci a sake musu abokansu da hukumomin tsaro suka kama.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel