Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger

Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger

- Wasu da ake kyautata zaton yan bindiga ne sun yi garkuwa da limamin Rigachikun, Kaduna

- Sheikh Mohammed Saminu Adam yana cikin motar haya ne da fasinjoji a hanyarsu na zuwa Niger daurin aure

- Sakataren kungiyar limamai da malamai na Kaduna ya tabbatar da lamarin inda ya ce an sanar da ƙungiyar

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace babban limamin masallacin Rigachikun a Kaduna, Sheikh Mohammed Saminu Adam, a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger.

A cewar Daily Trust, an sace malamin ne tare da wasu matafiya a yammacin ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu a babban titin Kaduna - Birnin Gwari.

DUBA WANNAN: Hotunan ɗalibar da ta tafi makaranta da bindiga za ta harbi malamin da ya ce ta aske gashinta mai launi

Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger
Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

An gano cewa malamin addinin na cikin motar haya ne tare da wasu fasinjoji a lokacin da aka kai musu harin.

Sakataren kungiyar limamai da malamai, reshen jihar Kaduna, Ustaz Yusuf Al'rigassiyu, ya tabbatar da lamarin inda ya ce an sanar da kungiyar.

KU KARANTA: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'

"Eh, mun ji labarin saboda mamba ne kuma an faɗa mana yan bindiga sun sace shi a hanyar Birnin Gwari," in ji shi.

Wani mazaunin Rigachikun wanda ya nemi a boye sunansa saboda ba a bashi izinin magana kan batun ba ya ce yan bindigan sun tuntubi iyalan limamin amma bai tabbatar idan sun fadi kudin fansa ba.

Mazaunin ya ce an sanar da labarin dace malamin yayin hudubar sallar Juma'a.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar ASP Mohammed Jalige ya ce bai da masaniya kan batun.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164