Daliban Kagara: Ba zan biya N500m da suke nema kudin fansa ba, gwamna Niger ya jaddada

Daliban Kagara: Ba zan biya N500m da suke nema kudin fansa ba, gwamna Niger ya jaddada

- Yanbindigan da suka sace daliban Kagara sun bukaci kudin fansa

- Hakazalika sun bukaci gwamnati ta saki wasu daga cikin abokansu dake hannunta

- Gwamnan jihar Neja ya ce ba zai amsa bukatunsu ba

A ranar Alhamis, har an fara sa ran sako dalibai da malaman makarantar GSC Kagara da aka sace, amma aka samu cikas saboda yan bindigan sun tsaya kan bakansu cewa sai an biya kudin fansa N500 million.

Sun bukaci wannan kudi ne matsayin kudin fansan matafiyan motar NSTA da suka sace, da kuma mutane 42 na makarantar GSC Kagara, Thisday ta ruwaito.

Yan bindigan sun kai hari makarantar ne ranar Laraba, inda suka kashe dalibi daya..

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, wanda ke cikin mutanen da ke tattaunawa da yan bindigan ya ce sun bukaci a sake musu abokansu da hukumomin tsaro suka kama.

Jami'an tsaro sun gano cewa an ajiye daliban ne a dajin Dutesn-Magaji dake karamar hukumar Rafi.

Gwamna Bello ya jaddada cewa ba zai biya yan bindigan kudi ba, kuma wajibi ne su sake mutanen da ke hannunsu.

Ya bayyana cewa ya fadi hakan ne saboda ya lura cewa da wannan kudi da ake basu suke amfani wajen sayan makaman da suke addaban mutane da shi.

Gwamnan ya ce shirya yake da baiwa yan bindigan sabon rayuwa muddin suka ajiye makamansu.

DUBA NAN: Ina so na iya Turanci sosai, ‘yar shekara 50 da ta shiga JSS2 ta magantu

Daliban Kagara: Ba zan biya N500m da suke nema kudin fansa ba, gwamna Niger ya jadda
Daliban Kagara: Ba zan biya N500m da suke nema kudin fansa ba, gwamna Niger ya jadda
Source: UGC

DUBA NAN: Kuma dai! Yan bindiga sun sake kaiwa mutane hari jihar Neja

A bangare guda, shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba 'yan fashi da ke son yin sulhu idan har za a magance matsalar tsaro a yanzu.

Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin ganawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.

Wannan ya faru ne bayan malamin ya ziyarci sansanin wasu yan fashi da ke aiki a jihar Neja.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel