Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe makiyayi da direban roka a Kaduna, in ji Kwamishina
- Yan bindiga a jihar Kaduna sun halaka wani makiyayi da kuma direban babban mota
- Yan bindigan sun bindige makiyayin ne sun sace babur dinsa yayin da suke tserewa jami'an tsaro
- Shi kuma direban motan yan bindigan sun harbe shi ne a yayin da suka tare hanyar kauyen Garawa
Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kashe makiyayi da direban babban mota a Kajuru, Karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, a cewar Mr Samuel Aruwan, Kwamishinan tsaro da harkokin gida, Vanguard ta ruwaito.
Da ya ke tabbatar da lamarin cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, Aruwan ya ce yan bindigan suna tserewa su koma cikin daji ne a kusa da kauyen Doka a karamar hukumar Kajuru, suka kashe makiyayin suka dauke babur dinsa da wasu kayayaki.
Ya yi bayanin cewa jami'an tsaro na bin sahun yan bindigan, yayin da an dauko gawar makiyayin an mika wa iyalansa don su yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.
DUBA WANNAN: Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger
'Yan bindigan ne suka garkuwa da kashe mutane a Kasuwan Magani da Doka da wasu wurare kusa da karamar hukumar Kaura.
"Kazalika, yan bindigan sun kashe wani direban babban mota a karamar hukumar Giwa," in ji Aruwan.
Ya ce rahoton tsaron da ake aike wa ma'aikatarsa ya ce lamarin ya faru kimanin awanni 48 da suka gabata yayin da yan bindigan suka datse hanyar kauyen Garawa suka bude wuta kan babban motar da ke dauke da rake daga kasuwan da ake ci mako-mako a jihar da ke makwabtaka da Kaduna.
KU KARANTA: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'
"Direban ya mutu nan take sakamakon harbinsa da bindiga da suka yi yayin da mataimakinsa na asibiti yana jinyar rauni," in ji shi.
Kwamishinan ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya nuna bakin cikinsa kan rasuwar makiyayin da direban inda ya yi addu'ar Allah ya jikansu.
Ya kuma yi wa wanda ya yi rauni fatan samun sauki cikin gaggawa.
A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.
A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.
A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng