Wani matashi ya dabawa tsohuwar budurwarsa wuka gaban kotu a jihar Adamawa

Wani matashi ya dabawa tsohuwar budurwarsa wuka gaban kotu a jihar Adamawa

- Wani matashi ya dabawa tsohuwar budurwarsa wuka a gaban kotu bayan wani hukunci

- Kotun ta yanke wani hukunci tsakaninsa da budurwar ne da bai wa shi matashin dadi ba

- 'Yan sanda sun kame matashin, yayin da aka wuce da ita budurwar asibiti domin bata kulawa

Wata kara da aka shigar tsakanin wani mutum da tsohuwar masoyiyarsa a garin Yola na jihar Adamawa, ta dauki hankali bayan da mutumin ya zaro wuka ya dabawa matar a gaban kotu.

Wanda ake zargin ya nuna cewa ya fusata da hukuncin Kotun Yankin Masu Laifi na 11 dake Yola, na sauya yarjejeniyar magana da matar ta yi na biyan N85, 000 ga mutumin bayan sun goyi bayan shirin aurensu.

Enoch Adamu ya maka Ashini Hosea a kotu kan neman a biyashi kudin. Ya so a dawo masa da duk kudin da ya ce ya kashe kan Ashini wanda ya janye daga shirin aurensu. Kudin sun hada da kudin baiko.

KU KARANTA: Yanzun nan: Sheikh Gumi ya rokawa 'yan bindiga gafara daga gwamnatin tarayya

Wani matashi ya dabawa tsohuwar budurwarsa wuka gaban kotu a jihar Adamawa
Wani matashi ya dabawa tsohuwar budurwarsa wuka gaban kotu a jihar Adamawa Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Ashini ta amince zata dawo da N85000. Duk da haka, kotun ta soke biyan kudin a ranar Alhamis.

Hukuncin kotun bai yi wa Adamu dadi ba wanda ya dauki wuka ya dabawa tsohuwar masoyiyar tasa.

An garzaya da Ashini asibiti don yi mata magani yayin da aka kama Adamu kuma aka kulle shi a sashen binciken manyan laifuka na ‘yan sanda (CID).

Duk da haka, wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin tserewa daga hannun 'yan sanda. Ya yi tsalle daga inda aka ajiye shi domin ya sauka kasa.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnan Neja ya karyata jita-jitan cewa an sako daliban GSSS Kagara

Wata majiyarmu ta ce ya suma ne kuma an garzaya da shi asibitin tarayya da ke Yola inda Ashini ke jinya.

Tuni lauyan Ashini ya bukaci kotu ta mayarwa Adamu kudinsa da ya bukata, yayin da kotun ta amince kuma ta bada umarnin ci gaba da rike Adamu.

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a Adamawa, a ranar Lahadi, ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da zama mamba a wata kungiyar gungun masu laifi da aka fi sani da‘ Shila Boys' a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa.

Wasu ‘yan zanga-zanga sun kona dan kungiyar Shila har lahira bisa zargin cewa ya yi wa wata mata sata da kuma daba mata wuka, Daily Trust ta ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.