Jama'ar gari sun cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola

Jama'ar gari sun cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola

- Wasu fusatattun jama'ar gari sun afkawa wani da ake zargi da aikata fashi da makami a Yola

- Mutanen sun samu nasarar cinna wa dan fashin wuta kuma ya kone kurmus har lahira

- Rundunar 'yan sandan Adamawa ta tabbatar da farruwar haka, kuma sun dauki gawar wanda aka kashen

Rundunar ‘yan sanda a Adamawa, a ranar Lahadi, ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da zama mamba a wata kungiyar gungun masu laifi da aka fi sani da‘ Shila Boys' a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa.

Wasu ‘yan zanga-zanga sun kona dan kungiyar Shila har lahira bisa zargin cewa ya yi wa wata mata sata da kuma daba mata wuka, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a jihar, DSP, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Yola.

KU KARANTA: Scholarship: Likitoci mata 47 'yan jihar Kano sun dawo bayan kammala karatu a Sudan

Nguroje ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 7:00 na dare.

Ya ce an dauki gawar wanda ake zargin ne daga rundunar Jimeta da ke Jimeta.

Ya fadawa NAN cewa mambobin kungiyar su uku, suna kan keke ne yayin da suka yi wa matar fashin a hanyar Mubi da ke Jimeta.

“Matar (an sakaya sunanta) ta yi ihu don neman taimako kuma nan take, wasu fusatattun mutane suka bi wadanda ake zargin, suka kama daya daga cikinsu suka cinna masa wuta.

“Sauran 'yan kungiyar biyu kuwa, sun tsere,’’ Nguroje ya fada wa NAN.

KU KARANTA: Gombe tana da mafi yawan wuraren kiwo a Afirka, in ji Gwamna Yahaya

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu masu satar mota su biyu a yankin Nassarawa na babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da aka fi sani da Western bypass, Daily Trust ta ruwaito.

‘Yan sanda sun kuma gano karamar mota kirar Toyota Camry dauke da lambar rajista ABC 590 DX da Toyota Corolla mai launin toka dauke da lambar rajista KTN 304 AG, daga wadanda ake zargin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel