Da dumi-dumi: Gwamnan Neja ya karyata jita-jitan cewa an sako daliban GSSS Kagara

Da dumi-dumi: Gwamnan Neja ya karyata jita-jitan cewa an sako daliban GSSS Kagara

- Gwamnan jihar Neja ya karyata wata jita-jita dake cewa an saki daliban GSSS Kagara

- Gwaman ya bayyana ana shirin tattauanwa da 'yan ta'addan don sako daliban da malamansu

- 'Yan sanda na ci gaba da sintiri don gano inda daliban suke da kuma kokarin ganin an ceto su

A jita-jita dake yawo a kafafen yada sada zumunta cewa an saki wasu dalibai da malamai na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara a jihar Neja, gwamnan jihar ya fayyace zahirin halin da ake ciki.

Gwamnan jihar ta Neja Abubakar Sani-Bello ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa an saki dalibai 27 da malamai 3 da aka sace a safiyar ranar Laraba a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara.

Ya ce gwamnati na matakin karshe na tattaunawa da 'yan fashin, yana mai alkawarin za a saki wadanda lamarin ya rutsa da su nan ba da dadewa ba.

KU KARANTA: Sace daliban Kagara: Sanata Shehu Sani ya aika sakon kar-ta-kwana ga gwamnan Neja

Da dumi-dumi: Gwamnan Neja ya karyata jita-jitan cewa an sako dalibanGSSS Kagara
Da dumi-dumi: Gwamnan Neja ya karyata jita-jitan cewa an sako dalibanGSSS Kagara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A jiya rahotanni daga Legit.ng Hausa sun bayyana cewa 'yan sanda sun gano alamar inda 'yan fashin suka boye tare da daliban da kuma sauran ma'aikatan makarantar da aka sacen, sai dai ba a samu labarin cewa 'yan sanda sun afka wa wurin ba.

Hakazalika, wani babban malamIN addinin Islama ya gana da gwamnan kan yadda za a bi don ceto daliban da malamansu.

Bayan ganawa da gwamnan, malamin ya zarce kai tsaye zuwa kungurmin daji domin ya gana da shugabannin 'yan ta'addan; wanda hakan ya jawo wasu ke ganin kamar an sako wasu daga cikin daliban ne.

KU KARANTA: Yanzun nan: Sheikh Gumi ya rokawa 'yan bindiga gafara daga gwamnatin tarayya

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara aikin ceto ta sama don ceto daliban da aka sace, malamai, da sauran ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara.

Kakakin ‘yan sanda, Frank Mba, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa mai taken: Satar Kagara: Mun dukufa wajen ganin mun kubutar da duk wadanda aka sace, in ji IGP’, a ranar Alhamis.

Mba ya kuma ce tuni aka fara sa ido a iska don ganin an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.