2023: Tsohon gwamna ya bude wani babban sirri, ya ce nan ba da dadewa ba Wike zai koma APC

2023: Tsohon gwamna ya bude wani babban sirri, ya ce nan ba da dadewa ba Wike zai koma APC

- Babban mai tsawatarwa a majalisar dattijai, Orji Kalu, ya tabbatarwa mambobin jam’iyyar APC cewa nan ba da jimawa ba Wike zai dawo jam’iyya mai mulki

- Kalu ya bayyana hakan ne a Port Harcourt a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairu, yayin duba wani aiki

- Tsohon gwamnan na Abia ya kara da cewa ya sami tattaunawa mai kyau da Wike yayin ziyarar sa a jihar Ribas

Babban bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu ya ba mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tabbacin cewa Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, zai dawo jam’iyyar mai mulki nan ba da dadewa ba.

Kalu ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan Wike ya jagorance shi a yayin duba wani aiki a Port Harcourt, babban birnin jihar a ranar Alhamis, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Tattalin arziƙin Nigeria ya farfaɗo, an samu ƙarin kaso 0.11

2023: Tsohon gwamna ya bude wani babban sirri, ya ce nan ba da dadewa ba Wike zai koma APC
2023: Tsohon gwamna ya bude wani babban sirri, ya ce nan ba da dadewa ba Wike zai koma APC Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Wasu daga cikin ayyukan da aka duba sun hada da gadar sama na Rumuokoro, gadar sama na biyu na Artillery, makarantar kwallon kafa na Real Madrid da kuma asibitin Mother and Child Hospital a Rumuomasi.

“Wike mutum ne da muke buƙata a cikin APC, na yi imani cewa almasihu zai iya zuwa daga ko'ina.

“Ina rokon Gwamnan da ya hada kai da APC, na tattauna da shi duk tsawon dare don gano bakin zare tare da APC. Na yi imanin cewa ba da daɗewa ba zai zama gaskiya.

“Don haka ina kira ga Gwamna Wike da ya sassauta wa jam’iyyarmu, mutane na iya sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan wacce dabi’ar mutum ce a Afirka..

“Ina kira gare shi da ya hada kai da mu domin mutanen kirki na Ribas su kara cin gajiyar Gwamnatin Tarayyar Najeriya,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Auwal Daudawa: Na jagoranci sace yaran Kankara ne saboda Gwamna Masari ya tabo mu

A wani labarin, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira da cewa a sallami Ministan Tsaro, Manjo janar Bashir Magashi daga aikinsa ba tare da bata lokaci ba saboda rashin yin aikinsa, Daily Trust ta ruwaito.

Jam'iyyar cikin sanarwar da sakataren watsa labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce ta bukacin hakan ne furucin da ya yi na cewa jama'ar Nigeria marasa makamai su kare kansu daga hare-haren yan bindiga da yan ta'adda.

Sanarwar ta PDP ta ce irin wannan yunkurin kauce sauke nauyi na gwamna alama ne da ke tabbartwa cewa Nigeria na neman zama kasar da ta gaza a karkashin gwamnatin Buhari tunda gwamnati ba za ta iya aikinta ba na maganin yan bindiga da masu tada kayan baya.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel