Ba duka yan bindiga bane mutanen banza: Gwamnan Zamfara

Ba duka yan bindiga bane mutanen banza: Gwamnan Zamfara

- Gwamnan Matawalle ya amsa sammacin shugaba Muhammadu Buhari

- Gwamnan Zamfaran ya ziyarci shugaban kasan a fadarsa dake Aso Villa ranar Alhamis

- Matawalle ya bayyana cewa rashin adalci ya tilastawa yan bindiga fito-na-fito da gwamnati

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ba duka tsagerun yan bindiga bane mutanen banza, wasu kawai dole ce ta wajabta musu daukar bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 18 ga Febrairu, 2021, Vanguard ta ruwaito

Ya yi bayanin cewa yawancin yan bindigan sun shiga harkar ne saboda irin rashin adalcin da al'ummar gari ke musu.

"Ba dukkansu bane mutanen banza. Idan ka bincike abinda ke faruwa, da kuma abinda ya sa suka dauki doka a hannunsu, wasu daga cikinsu sun fuskanci zalunci ne daga wajen yan banga," Matawalle yace.

"Su (Yan bangan) kan kai musu hari a rugarsu, su lalata musu dukiya kuma su kwashe musu dabbobi. Babu wanda zasu kai wa kara, shi yasa wani lokaci suke daukan fansa."

"Wasunsu na zama da kauyuka kusa da gari. Duk lokacin da Sojoji suka kai hari, su kan lalata musu dukiya da dabbobi. Suna jin haushin wadannan abubuwa. Idan ka tattauna da su, za ka fahimci wadannan abubuwa."

KU KARANTA: Buratai da sauran tsaffin hafsoshin tsaro sun dira majalisa

Ba duka yan bindiga bane mutanen banza: Gwamnan Zamfara
Ba duka yan bindiga bane mutanen banza: Gwamnan Zamfara Credit: Presidency
Asali: Twitter

DUBA NAN: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa

A bangare guda, Auwal Daudawa, wanda ya jagoranci sace daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kankara, Jihar Katsina, ya ce ya jagoranci wannan samamen ne saboda Gwamna Bello Masari ya kuskurewa dakarunsa.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust, Daudawa ya ce ya so tabbatar wa da gwamnati cewa yana da karfin da zai kai irin wannan harin.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel