Sace daliban Kagara: Sanata Shehu Sani ya aika sakon kar-ta-kwana ga gwamnan Neja

Sace daliban Kagara: Sanata Shehu Sani ya aika sakon kar-ta-kwana ga gwamnan Neja

- A ci gaba da hare-hare a yankin arewacin Najeriya, jama'a sai tofa albarkacin bakinsu suke

- Ba a bar sanata Shehu Sani a baya ba, shima ya yi tsokaci kan sace 'yan makarantar Kagara

- Ya ta'allaka sace yaran da ganganci da kuma sakacin rashin gyara kantangar makarantar

Biyo bayan hari da kuma sace dalibai da ma'aikatan makarantar Kagara dake jihar Neja, masana harkokin siyasa, tsaro da lamuran yau da kullum sai fadan albarkacin bakinsu suke.

Daya daga cikinsu, wani tsohon sanata a jihar Kaduna, Shehu Sani da ya shahara wajen sharhi kan lamuran siyasar yau da kullum, ya tofa albarkacin bakinsa dangane sace daliban, yana mai sharhi kan yadda yanayin ginin makarantar yake.

Shehu Sani ya wallafa wata magana a shafinsa na Twitter da ke nuna damuwarsa ga yadda lalacewar ginin GSSS Kagara yake, yana mai shawartar gwamnan jihar a kai-kaice.

KU KARANTA: Shawarin Atiku: Ya kamata a tura jami'an sojoji kowace makaranta a kasar

Rashin gyara ne ya sanya aka sace dalibai GSSS Kagara, Shehu ga gwamnan Neja
Rashin gyara ne ya sanya aka sace dalibai GSSS Kagara, Shehu ga gwamnan Neja Hoto: @ShehuSani
Asali: Twitter

Ya bayyana sace yaran makarantar a masatyin wani darasi da gwaman jihar Neja ya kamata ya koya domin inganta fasalin makarantu a fadin jihar ta Neja, ciki har da GSSS Kagara.

Shehu ya bayyana cewa bala'i da iftila'i yakan zama damar da mutum zai gyara kuskurensa; saboda haka alheri ne.

Da fadin haka sai ya shawaric gwamnan da ya "Yi amfani da wannan damar don sake gina GSC Kagara, bayan an kwashe shekaru da yawa ba a kula da shi ba."

Harshe ya bayyanawa gwamnan cewa sakacin rashin gyara makarantar ne ya jawo aka sace mutanen.

"Rashin shingen da ya kewaye makarantar ne yasa hakan ya zama da sauki ga masu satar mutane. Makarantun gwamnati bai kamata su zama shingen hayewa ga 'yan fashi da 'yan ta'adda ba. In ji Shehu Sani.

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya isa jihar Neja zai kuma zarce jihar Kebbi don tattauna matsalar tsaro

A wani labarin, A ci gaba da sace-sacen daliban makaranta da malamansu da ke faruwa a arewacin Najeriya, tsoro da firgici na shiga zukatan mutane tare da nuna alamar tambayar 'shin akwai isasshen tsaro da zai iya amintar da iyaye su yarda su tura 'ya'yansu makaranta?'

Gwamnatin tarayya da ta jihohin arewa na cikin tashin hankali dangane da tabarwarewar tsaro, sai dai wasu masu ta cewa a lamuran yau da kullum na ganin akwai gazawar gwamnati da kuma rashin kwarewar jami'an tsaro wajen shawo kan lamarin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel