Tsoron sace dalibai: Gwamnatin jihar Osun ta garkame makaranta

Tsoron sace dalibai: Gwamnatin jihar Osun ta garkame makaranta

- Gwamnatin jihar Osun ta garkame wata makaranta sakamakon barazar kai hari a cikinta

- Jihar ta bayyana hakan a matsayin matakin farko na dakile rikicin da ake tunani zai afku

- Hakazalika jihar ta kirayi iyaye da masu ruwa da tsaki su kula da sanarwar gwamnatin jihar

Gwamnatin jihar Osun a ranar Alhamis ta sanar da cewa za a rufe makarantar lfeoluwa Grammar School Osogbo sakamakon mamaya da wasu ‘yan daba dauke da makamai suka yi a harabar makarantar.

Majiya ta tabbatar da lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata, 16 ga watan Fabrairu, 2021, da misalin 11:45 na safe lokacin da wasu ‘yan daba dauke da makamai suka mamaye makarantar, lamarin da ya haifar da rikici a makarantar.

Wani shaidar gani da ido, ya ce, “Yaran Egbatedo wadanda yawansu ya kai kimanin ashirin sun mamaye makarantar, suna ta barazana da adduna da wasu makamai.

KU KARANTA: Shawarin Atiku: Ya kamata a tura jami'an sojoji kowace makaranta a kasar

Tsoron sace dalibai ya sa gwamnatin wata jiha ta garkame makaranta
Tsoron sace dalibai ya sa gwamnatin wata jiha ta garkame makaranta Hoto: Premium Times
Source: UGC

"Sun kori ma'aikata da daliban daga harabar makarantar tare da barazanar kai musu hari. Ba a san dalilan da yasa suke haka ba.

“Mutum daya ya yanke da adda kuma an dauke shi zuwa asibiti kafin isowar 'yan sanda wurin. Amma ‘yan sanda sun cafke daya daga cikin wadanda ake zargin.”

Sakamakon haka, wata sanarwa daga Daraktan Gudanarwa na Ma’aikatar Ilimi, Misis Kehinde Olaniyan, ta sanar da rufe makarantar a ranar Alhamis.

Ta ce, “Wannan an sanar da shi ne ga jama’a musamman iyaye, masu kula da daliban da ke makarantar lfeoluwa Grammar School Osogbo, cewa mai girma Kwamishinan Ilimi ya ba da umarnin a rufe Makarantar na wani lokaci har sai wani lokaci.

Sanarwar ta bayyana daukar matakin rufe makarantar a matsayin shawo kan rikicin da kan iya faruwa da dalibai da kuma ma'aikatan makarantar.

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya isa jihar Neja zai kuma zarce jihar Kebbi don tattauna matsalar tsaro

A wani labarin, A ci gaba da sace-sacen daliban makaranta da malamansu da ke faruwa a arewacin Najeriya, tsoro da firgici na shiga zukatan mutane tare da nuna alamar tambayar 'shin akwai isasshen tsaro da zai iya amintar da iyaye su yarda su tura 'ya'yansu makaranta?'

Gwamnatin tarayya da ta jihohin arewa na cikin tashin hankali dangane da tabarwarewar tsaro, sai dai wasu masu ta cewa a lamuran yau da kullum na ganin akwai gazawar gwamnati da kuma rashin kwarewar jami'an tsaro wajen shawo kan lamarin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel