Rashin nuna kwarewar jami'an tsaro ke jawo sace dalibai, in ji Solomon Dalong
- Hon. Solomon Dalong ya bayyana cewa jami'an tsaro suna nuna gazawa wajen gudanar da aikinsu
- Ya nuna damuwarsa kan yadda hare-hare ke ci gaba da faruwa a yankin arewacin Najeriya
- Ya kuma bayyana dalilan da yasa hare-haren ke ci gaba da sakaci irin na jami'an tsaro
A ci gaba da sace-sacen daliban makaranta da malamansu da ke faruwa a arewacin Najeriya, tsoro da firgici na shiga zukatan mutane tare da nuna alamar tambayar 'shin akwai isasshen tsaro da zai iya amintar da iyaye su yarda su tura 'ya'yansu makaranta?'
Gwamnatin tarayya da ta jihohin arewa na cikin tashin hankali dangane da tabarwarewar tsaro, sai dai wasu masu ta cewa a lamuran yau da kullum na ganin akwai gazawar gwamnati da kuma rashin kwarewar jami'an tsaro wajen shawo kan lamarin.
Hon. Solomon Dalung, wani jigo a siyasar Najeriya, ya yi sharhi dangane da yadda jami'an tsaron Najeriya ke gaza daukar mataki kafin faruwar lamarin sace-sacen mutane a arewacin Najeriya.
KU KARANTA: FG da jihar Neja na neman tattaunawa da wadanda suka sace daliban Kagara
Ya bayyana cewa, jami'an tsaron kan gaza wajen daukar darasi daga satar 'yan makaranta da aka yi a baya domin su kiyaye faruwar na gaba, wanda a hakan ne ya jawo sace wasu 'yan makarantar a Kankara a baya da kuma Kagara a jiya Laraba.
Dalung a wata hira da wakilinmu na Legit.ng Hausa ya bayyana cewa jami'an tsaron "basu nuna wani bajinta ko isahara da suka koya a cikin abinda ya faru a baya ba, domin kowane lokaci, duk sadda abu ya faru yakan zo musu ne a matsayin ba za ta."
Ya kuma bayyana hakan a matsayin rashin nuna kwarewar aiki da rashin kokarin tattara bayanai don kiyaye faruwar harin a nan gaba.
"Jami'an tsaron basa tattara bayanai na asiri na abubuwan da suka gabata ba domin suyi nazari su fitar da tsarin yadda za a fitowa abin a nan gaba ba. Wannan kuwa nuni ne cewa ya bayyana karara sun gaza." in ji shi.
KU KARANTA: Majiya ta shaida yadda aka sace dalibai da malaman GSSS Kagara
A wani labarin, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, a ranar Laraba cikin wata sanarwa, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya jami’an soji dauke da makamai a duk makarantun “don kariya awanni 24 a kwanaki 7.”
Atiku ya yi tir da sace dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara, Jihar Neja, a cikin wani rahoton Daily Trust.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng