Shawarin Atiku: Ya kamata a tura jami'an sojoji kowace makaranta a kasar

Shawarin Atiku: Ya kamata a tura jami'an sojoji kowace makaranta a kasar

- Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya ya shawarci gwamnati kan rashin tsaro

- Ya lura da cewa rashin tsari na bukatar daukar mataki nan take ba tare da bata lokaci ba

- Yace ya kamata gwamnati ta tura sojoji zuwa dukkan makarantun kasar saboda sato

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, a ranar Laraba cikin wata sanarwa, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya jami’an soji dauke da makamai a duk makarantun “don kariya awanni 24 a kwanaki 7.”

Atiku ya yi tir da sace dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara, Jihar Neja, a cikin wani rahoton Daily Trust.

Ya roki Gwamnatin Tarayya da ta bayyana dukkan makarantun sakandare da na firamare a jihohin da abin ya shafa a matsayin yankuna masu kariya na tarayya.

KU KARANTA: Bana son annobar Covid-19 ta kare, saboda a lokacinta na sayi jirgi na 3, in ji Fasto

Shawarin Atiku: Ya kamata a tura jami'an sojoji kowace makaranta a kasar
Shawarin Atiku: Ya kamata a tura jami'an sojoji kowace makaranta a kasar Hoto: BBC
Source: UGC

“Idan ba zai yiwu a samu sojoji masu dauke da makamai a dukkan makarantu ba, to kowace jiha a cikin gaggawa ya kamata ta kirkiri kungiyar hadin gwiwar 'yan kungiyar farar hula, tare da jami'an tsaron farin kaya.

“Abin da bai kamata mu yi ba shi ne yin komai. Tarihi na iya gafarta mana don yanke shawara mara kyau, amma ba za a taɓa gafarta mana ba idan muka ci gaba da kasuwanci kamar yadda muka saba.

"A matsayinmu na kasa, dole ne mu kasance a shirye don samar da tsaro irin wanda muke samarwa ga makarantun da yaran manyan mutane ke halarta ga makarantun da 'ya'yan talakawa 'yan Najeriya ke halarta."

Ya kuma ce: “Yawaitar rashin tsaro a Najeriya yanzu ya wuce abin misali. Ya kai ga matakan rikici, musamman idan abin ya shafi yara da sauran ƙananan yara.

“Yanzu ba lokaci bane da yatsu za su nuna zargi. Al'ummarmu suna bukatar mafita. Kuma yanzu mun ga cewa biyan fansa, da kuma barin masu laifi su ci riba daga aikata laifin ba shi ne mafita ba.

KU KARANTA: Buhari ya tura jami'an tsaro jihar Neja don su kwato daliban da aka sace

A wani labarin, Majalisar dattijai, a ranar Laraba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da, cikin gaggawa, ya sanya dokar ta baci kan tsaro sakamakon sace ma’aikata da dalibai a wata makaranta a Niger.

Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Muhammed Sani Musa (APC, Neja) ya gabatar wanda ya ja hankalin abokan aikinsa kan sace wasu dalibai da ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, Jihar Neja, da misalin karfe 2 na daren Laraba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel