Sheikh Gumi ya isa jihar Neja zai kuma zarce jihar Kebbi don tattauna matsalar tsaro

Sheikh Gumi ya isa jihar Neja zai kuma zarce jihar Kebbi don tattauna matsalar tsaro

- Shararren Malamin addinin Islama Sheikh Gumi ya isa jihar Neja don tattauna matsalar tsaro

- Malamin ya kuma bayyana cewa zai wuce jihar Kebbi don wata tattaunawar kan rashin tsaro

- Malamin ya bayyana cewa ya tattauna da gwamnan jihar Neja kan mafita ga rashin tsaro

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, malamin addinin musuluncin da ya shahara wajen tattaunawa da 'yan ta'adda a yankin Kaduna da Zamfara ya gana da gwamnan jihar Neja Abubakar Sani-Bello a ranar Laraba kan halin tsaro a jihar.

Gumi wanda ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Kebbi, ya shaida wa manema labarai bayan taron cewa: “Ni da gwamnan mun yi magana a kan hanyoyi da yawa don magance rashin tsaro ta hanyar da ta dace da kuma nemo hanyoyin magance matsalar rashin tsaro a jihar."

KU KARANTA: Shawarin Atiku: Ya kamata a tura jami'an sojoji kowace makaranta a kasar

Sheikh Gumi ya isa jihar Neja zai kuma zarce jihar Kebbi don tattauna matsalar tsaro
Sheikh Gumi ya isa jihar Neja zai kuma zarce jihar Kebbi don tattauna matsalar tsaro Hoto: Kanyi Daily
Source: UGC

Yayi alkawarin zuwa Kagara inda aka sace daliban. Gumi ya gana da 'yan fashi a jihohin Kaduna da Zamfara don lallashin su su yar da bindiga su rungumi zaman lafiya.

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa malamin ya shawarci jihohi kan yadda ya kamata su shawo kan rashin tsaro a jihohinsu ganin yadda lamarin hare-hare ya yawaita a arewacin Najeriya.

Wasu gwamnonin sun bi shawarin malamin, yayin da suka amince da yafewa 'yan ta'addan, yayin da wasu kuwa suke sukar ra'ayin nasa.

Malamin ya ci gaba da shiga dazuka domin tattaunawa da 'yan ta'adda da jin dalilansu na aikata ta'addanci. Ya kan kuma shawarcesu tare da yi musu nasiha su rungumi zaman lafiya da bin doka da oda.

KU KARANTA: FG da jihar Neja na neman tattaunawa da wadanda suka sace daliban Kagara

A wani labarin, Wani mazauni da ya shaida yadda aka sace dalibai 27 da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati 15, Kagara da ke cikin Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja, ya bayyana yadda masu garkuwar suka daure wadanda suka sace su bibbiyu suka tafi da su.

Mutumin, wanda ke zaune kusa da makarantar, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa ‘yan fashin, wadanda ke sanye da kayan sojoji, sun far wa makarantar da karfe 2 na dare.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel