Rashin tsaro: Gwamnan Arewa ya zargi takwarorinsa da yin sakaci da aikinsu

Rashin tsaro: Gwamnan Arewa ya zargi takwarorinsa da yin sakaci da aikinsu

- An zargi wasu gwamnonin arewa da yi wa lamarin rashin tsaro rikon sakainar kashi

- Zargin ya fito ne daga Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairu

- Bello ya ce da taimakon gwamnatinsa fashi da makami, rikicin makiyaya/manoma, da kowane irin rikici ya zo karshe a Kogi

A ra'ayinsa, Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya yi imanin cewa wasu gwamnonin Najeriya ba su mayar da hankali wajen magance matsalar rashin tsaro ba a jihohinsu.

Bello a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairu, ya yarda cewa a baya, Kogi ta kasance matattarar masu satar mutane, 'yan fashi, da' yan ta'adda, jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya yi iƙirarin cewa har yanzu wasu gwamnonin ba su ba da fifiko kan lamarin tsaro a jiharsu ba shi ya sa idan aka tattauna don yin musayar ra'ayoyi a kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ba a cimma sakamako da yawa.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: 'Yan fashi za su dandana kudarsu yayin da IGP ya tura dakaru na musamman 302 zuwa jihar Kaduna

Rashin tsaro: Gwamnan Arewa ya zargi takwarorinsa da yin sakaci da aikinsu
Rashin tsaro: Gwamnan Arewa ya zargi takwarorinsa da yin sakaci da aikinsu Hoto: @GovernorBello
Asali: Twitter

Gwamnan na Kogi ya ce bai yarda da rugawa wajen Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a duk lokacin da wata matsala ta taso a jiharsa.

Saboda haka ya yi kira ga gwamnoni a kasar da su tashi tsaye su kawo karshen wannan matsalar domin ba a bukatar ta kwata-kwata.

“NGF dandali ne na gwamnoni domin kwatanta ra'ayoyi amma, duk da haka, kwarewar da kuka raba a cikin NGF, zai dogara ne akan abunda kowannenmu ya fi bayar da muhimmanci a kai.

“Dole ne in fada kai tsaye cewa akwai wasu daga cikinmu da suka fi ba da mahimmanci a kan ayyukanmu. Ba zan kira sunaye ba, akwai wasu daga cikinmu da suke fifita ayyukanmu kuma suna yin sa sosai a jihohinmu daban-daban kuma wasu suna buga siyasa ne kawai, sannan ya kamata mu gaggauta dakatar da hakan. Mu rage nauyin da ke wuyan Shugaban kasa sannan kuma mu ceci rayukan mutanenmu."

KU KARANTA KUMA: Daliban Kagara: Ba 'yan fashi bane - Tsoro ya mamaye Neja yayin da sanata ya bayyana asalin masu satar mutane

A gefe guda, kasar Najeriya na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da sace-sacen mutane, fashi da makami, ta’addanci da dai sauransu.

A ranar Laraba, 17 ga watan Fabrairu ne aka wayi gari da labarin sace wasu dalibai a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Kagara, jihar Neja.

Wannan lamari ya jefa al’umman kasar musamman na jihar Neja cikin dimuwa, kasancewar wannan ba shine karo na farko da ake satar dalibai a kasar ba.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng