Siyasa ce ke rura wutar ta’addanci a Najeriya, Farfesa Taufiq AbdulAziz kan sace daliban Kagara

Siyasa ce ke rura wutar ta’addanci a Najeriya, Farfesa Taufiq AbdulAziz kan sace daliban Kagara

- Ana ci gaba da fuskantar matsalolin rashin tsaro a yankuna daban-daban na Najeriya

- Yan bindiga a ranar Laraba, 17 ga watan Fabrairu sun kai farmaki makarantar sakandare ta kimiyya ta gwamnati da ke Kagara, jihar Neja, sun sace dalibai da wasu ma'aikata

- Farfesa Taufiq AbdulAziz na jami'ar Abuja ya bayyana ra'ayinsa kan matsalar tsaro a kasar

Kasar Najeriya na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da sace-sacen mutane, fashi da makami, ta’addanci da dai sauransu.

A ranar Laraba, 17 ga watan Fabrairu ne aka wayi gari da labarin sace wasu dalibai a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Kagara, jihar Neja.

Wannan lamari ya jefa al’umman kasar musamman na jihar Neja cikin dimuwa, kasancewar wannan ba shine karo na farko da ake satar dalibai a kasar ba. Irin hakan ta faru a Chibok, Dapchi da Kankara, yanzu kuma a Kagara.

Siyasa ce ke rura wutar ta’addanci a Najeriya, Farfesa Taufiq AbdulAziz kan sace daliban Kagara
Siyasa ce ke rura wutar ta’addanci a Najeriya, Farfesa Taufiq AbdulAziz kan sace daliban Kagara Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Daliban Kagara: Ba 'yan fashi bane - Tsoro ya mamaye Neja yayin da sanata ya bayyana asalin masu satar mutane

Don haka Legit.ng ta tuntubi wani farfesa a jami’ar Abuja, Farfesa Taufiq AbdulAziz domin jin ra’ayinsa game da wannan matsala ta rashin tsaro da kasar ke fuskanta.

Farfesa Taufiq ya bayyana cewa lamarin siyasa na daya daga cikin mayan abubuwan da ke ta’azzara matsalar ta’addanci a Najeriya, inda ya ce a duk lokacin da ake shirin mika mulki, a kan yi amfani da matsalar tsaro da tattalin arziki musamman ta bangaren masu adawa.

A hirar da Legit Hausa ta yi da shi, Farfesan ya ce:

"A duk lokacin da ake shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati a Najeriya, mu kan lura da matsalolin rashin tsaro da na tattalin arziki.

"Wannan lokacin yana kama da gwamnatin yanzu tana samun nata kason ne kawai, lokacin da suke adawa, suma sunyi amfani dashi.

"Ka tuna suma sun yi amfani da Boko Haram, har ta kai ga Boko Haram ta zama rikici kuma abun kunya da ta kai har yankuna da dama a arewacin Najeriya sun zama ba Najeriya ba, domin ana ikirarin cewa kungiyar Boko Haram ta cinye su da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Majiya ta shaida yadda aka sace dalibai da malaman GSSS Kagara

"Abun ya yi muni matuka a lokacin zabe, dole sai da aka dage shi, kuma yayin dage zaben sai rikicin ya lafa kadan kuma ana ta ganin cewa rikice-rikicen za su tafi bayan zaben.

"Amma sai rikicin yaki karewa saboda yadda sakamakon zaben ya zo ba yadda aka yi tsammani ba. Ba za mu iya cewa ga ainahin abunda ya faru ba amma abin da ya ke gaskiya shi ne cewa siyasa ce ke haddasa shi."

A wani labarin, Gwamnatin tarayya da ta jihar Neja suna amfani da wani bangare na daban don tuntuɓar gungun 'yan fashin da suka sace 'yan makaranta da malamansu a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara.

'Yan bindigar sun mamaye makarantar ne da sanyin safiyar Laraba kuma suka tafi tare da wasu dalibai, ma'aikata da iyalansu.

Majiyar Daily Trust da ke da masaniya kan kokarin kubutar da wadanda aka sace din na Kagara, wadanda suka nemi a sakaya sunansu saboda mahimmancin batun, sun bayyana wa majiya cewa an yanke shawarar yin amfani da hanyoyin kofar waje don sakin wadanda aka sacen.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel