FG da jihar Neja na neman tattaunawa da wadanda suka sace daliban Kagara
- Gwamnatin tarayya tare da ta Neja na kokarin ceto yara da malamai na GSSS Kagara
- Gwamnatin a wata majiya tana amfani da tsoffin 'yan ta'adda don ceto wadanda aka sacen
- Sannan gwamnati ta kara tsaurara tsaro a yankin na jihar Neja don ceto yara da malaman
Gwamnatin tarayya da ta jihar Neja suna amfani da wani bangare na daban don tuntuɓar gungun 'yan fashin da suka sace 'yan makaranta da malamansu a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara.
'Yan bindigar sun mamaye makarantar ne da sanyin safiyar Laraba kuma suka tafi tare da wasu dalibai, ma'aikata da iyalansu.
Majiyar Daily Trust da ke da masaniya kan kokarin kubutar da wadanda aka sace din na Kagara, wadanda suka nemi a sakaya sunansu saboda mahimmancin batun, sun bayyana wa majiya cewa an yanke shawarar yin amfani da hanyoyin kofar waje don sakin wadanda aka sacen.
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Bazan biya kudin fansa ba ko kobo, Gwaman Neja
Daya daga cikin majiyar ta ce jami'ai sun tuntubi wasu shugabannin Fulani da tubabbun 'yan ta'adda wadanda suka tuntubi 'yan fashin don tattaunawa a kan sakin wadanda lamarin ya rutsa da su.
An tattaro cewa wasu tubabbun Fulani 'yan fashin da suka fito daga jihohin Katsina da Zamfara an shirya su domin tunkarar masu garkuwar.
“Tuni wasu nasarori suka samu. Mun sami damar tabbatar da cewa wadanda suka sace yaran Fulani ne daga daya daga cikin sansanonin da ke cikin dazuzzukan Kaduna, wadanda suka yi iyaka da Neja zuwa kudanci da kuma Zamfara zuwa arewa.” in ji daya daga cikin majiyar.
“Amma babbar dambarwar yanzu shine sa su yarda cikin sauki saboda a Kaduna babu yarda tsakanin yan fashin da gwamnati.
"Amma mutanen da abin ya shafa suna aiki kan samar da hanyar da za su zauna da shugabannin wadanda suka sace su, dattawan da za su iya tilasta musu su bi wannan bukata, ”inji shi.
Wani babban jami’in tsaro ya ce an tsaurara matakan sintiri ta sama a kan iyakokin da ke tsakanin Kaduna da jihar Neja.
KU KARANTA: Bana son annobar Covid-19 ta kare, saboda a lokacinta na sayi jirgi na 3, in ji Fasto
A wani labarin, Majalisar dattijai, a ranar Laraba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da, cikin gaggawa, ya sanya dokar ta baci kan tsaro sakamakon sace ma’aikata da dalibai a wata makaranta a Niger.
Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Muhammed Sani Musa (APC, Neja) ya gabatar wanda ya ja hankalin abokan aikinsa kan sace wasu dalibai da ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, Jihar Neja, da misalin karfe 2 na daren Laraba.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng