An kashe mana mutane sama da 23 a rikicin Ogun, in ji Sarkin Fulani

An kashe mana mutane sama da 23 a rikicin Ogun, in ji Sarkin Fulani

- Sarkin Fulanin Abeokuta ya koka kan yadda ake hallaka Fulani makiyaya a yankin na Ogun

- A cewarsa, mutane sama da 23 aka kashe ba tare da wani hakki ba, bayan kona gidaje da dama

- Shugaban kungiyar Miyetti Allah shima ya koka kan yadda ake kallon makiyaya da ta'addanci

Sarkin Fulanin Abeokuta, Muhammad Kabir Labar a ranar Talata ya ce an kashe makiyaya 23 tare da kona gidaje kimanin 20 a rikicin kwanan nan a Jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi magana a taron masu ruwa da tsaki kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawale, gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu da gwamnan jihar Neja Abubakar Sanni Bello.

Ya ce wasu mutane sun jajirce kan “nuna adawa da juna ta hanyar yin amfani da bambance-bambancen kabilanci.”

KU KARANTA: Gamayyar gwamnoni tayi alkawarin tallafawa Makinde a sake gina kasuwar Sasha

An kashe mana mutane sama da 23 a rikicin Ogun, in ji Sarkin Fulani
An kashe mana mutane sama da 23 a rikicin Ogun, in ji Sarkin Fulani Hoto: Premium Times
Source: UGC

Rikicin kwanan nan tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankunan da ke cikin rikici na Yewaland ya yi sanadiyyar rayukan mutane a Eggua, Ketu, Igbooro, Iselu, Agbon-Ojodu, Asa, Ibeku, Imeko da Oja-Odan.

Labar ya dora alhakin rikicin kan “baƙi” waɗanda, in ji shi, suka kawo cikas ga zaman lafiyar da ake mora a cikin jihar tsawon shekaru.

Shugaban kungiyar makiyaya na Miyetti Allah ta Najeriya, Muhammad Kirowa, ya ce makiyaya ba masu tayar da hankali ba ne, illa wadanda harin ya shafa.

Ya ce sama da shanu 8,000 ne ake amfani da su a Kudu maso Yamma a kowace rana.

“Mutanenmu sun fi shan wahala a hannun masu laifi a Najeriya. Amma an nuna mu a matsayin masu laifi. Makiyayan sun cancanci jin kai. Ba masu laifi bane," in ji shi.

KU KARANTA: Idan Fani Kayode ya koma APC, to PDP ce zata ruguje ba shi ba, in ji jigon PDP

A wani labarin, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnoni hudu daga yankin arewacin Najeriya a yanzu haka suna ganawa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Taron ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabanin Fulani, manoma da sarakunan gargajiya a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel